1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce

عَنْ أَبِي الحَوْرَاءِ السَّعْدِيِّ قَالَ: قُلْتُ لِلْحَسَنِ بْنِ عَلِيٍّ رضي الله عنهما: مَا حَفِظْتَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؟ قَالَ: حَفِظْتُ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«دَعْ مَا يَرِيبُكَ إِلَى مَا لاَ يَرِيبُكَ، فَإِنَّ الصِّدْقَ طُمَأْنِينَةٌ، وَإِنَّ الكَذِبَ رِيبَةٌ».

Daga Abul Haura'u al-Sa'adi ya ce: Na cewa Hassan ɗan Ali - Allah Ya yarda da su -: Me ka haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -? ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:
"Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce".

Ingantacce ne Tirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shi Sunan Tirmizi - 2518

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abinda kake kowanto a cikinsa na maganganu da ayyuka cewa shi an hana ne koko a'a, shin shi haramun ne ko halal ne, zuwa abinda babu kokwanto a cikinsa daga abinda ka sakankance kyansa da kuma halaccinsa, domin cewa zuciya zata nutsu gare shi ta samu kwanciyar hankali, abinda kuma a cikinsa akwai kokwanto to zuciya tana kaikawo daga gareshi kuma tana raurawa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ya wajaba akan musulmi ya gina al'amuransa akan yaƙini da barin abinda ake kokwanto a cikinsa, kuma ya zama mai basira akan Addininsa.
  2. Hani daga afkawa cikin shubuhohi.
  3. Idan kana son nutsuwa da hutu to kabar abinda ake kokwanto a cikinsa ka jefar da shi a gefe.
  4. Rahamar Allah ga bayinSa, dan Ya umarcesu da abinda a cikinsa akwai hutun rai da zuciya, kuma ya hanesu daga abinda a cikinsa akwai raurawar zuciya da kuma ɗimuwa.

Manufofin Fassarorin

60 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو