1. Gida
  2. kashe kashe
  3. SIRA DA TARIHI

Sabuntawa Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira

عَنْ أبي سَلَمَةَ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ أَنَّ جَابِرَ بْنَ عَبْدِ اللَّهِ الأَنْصَارِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: وَهُوَ يُحَدِّثُ عَنْ فَتْرَةِ الوَحْيِ، فَقَالَ فِي حَدِيثِهِ:
«بَيْنَا أَنَا أَمْشِي إِذْ سَمِعْتُ صَوْتًا مِنَ السَّمَاءِ، فَرَفَعْتُ بَصَرِي، فَإِذَا المَلَكُ الَّذِي جَاءَنِي بِحِرَاءٍ جَالِسٌ عَلَى كُرْسِيٍّ بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، فَرُعِبْتُ مِنْهُ، فَرَجَعْتُ فَقُلْتُ: زَمِّلُونِي، فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَعَالَى: {يَا أَيُّهَا المُدَّثِّرُ1 قُمْ فَأَنْذِرْ} [المدثر: 2] إِلَى قَوْلِهِ {وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ} [المدثر: 5]. فَحَمِيَ الوَحْيُ وَتَتَابَعَ».

Daga Abu Salama Ibnu Abdurrahman cewa Jabir Ibnu Abdullahi al-Ansari - Allah Ya yarda da su - ya ce: Alhali shi yana bada labari game da lokacin wahayi, a cikin zancensa sai ya ce:
"Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira a zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, ai na ji tsoronsa, sai na dawo sai na ce: Ki lulluɓeni, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da {Ya kai mai lulluɓa1 Ka tashi ka yi gargaɗi}[alMuddasir: 2] zuwa faɗinSa: {Ka ƙauracewa gumaka} [al-Muddassir: 5]. Sai wahayi ya tsananta kuma ya bibiyi juna.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 4

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari alhali shi yana bada labari game da tsayawar wahayi da kuma dakatar da saukarsa a farkon manzancinsa: Wata rana ina tafiya a lungun Makka sai na ji wata ƙara daga sama sai na ɗaga idona, sai ga mala'ikan da ya zo mini a kogon Hira yana zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, sai na tsorata na razana daga gare shi, sai na dawowa iyalina sai na ce: Ku lulluɓeni da tufafi. Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da: {Ya kai mai lulluɓa} mai lulluɓa da tufansa, {Ka ta shi} da kira {Ka yi gargaɗi} ka gargaɗar da wanda bai yi imani da saƙonka ba. {Ubangijinka} Ubangijinka abin bauta {Ka girmama} ka gode maSa ka girmamaShi. {Tufafinka} tufafinka {Ka tsarkake} ka tsamosu daga najasa, {Gumaka} da bautar gumaka da mutun mutumi {To ka ƙaurace} ka bari, sai wahayi ya yi ƙarfi bayan haka ya yi yawa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Yankewar wahayi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bayan saukar faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Ka yi karatu}.
  2. Halaccin mutum ya bada labarin abin da ya faru gare shi na jarawaba bayan gushewar jarabawar, dan godiya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
  3. Farkon abin da ya sauka shine faɗinSa: {Yakai mai lulluɓa} bayan saukar: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta}.
  4. Falalar Allah - tsarki ya tabbatara maSa Ya ɗaukaka - ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda ya zuba wahayinSa ba tare da yankewa ba har sai da yabar duniya.
  5. Wajabcin tsayuwa da kira zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da yi wa waɗanda suka bijire gargaɗi da yi wa masu biyayya albishir.
  6. Wajabcin tsarkake tufafi dan yin sallah, haƙiƙa sun kafa hujja da faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Ka tsarkake tufafinka}.
  7. Wajabcin yin imani da mala'iku da kuma abin da Allah Ya basu iko a kansa na ayyuka da wasunsu.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية