1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Da a ce za ku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro, da Ya azurtaku kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace kuma ya yi yammaci a ƙoshe

عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: إنه سمع نبي الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«لَو أَنَّكُمْ تَتَوَكَّلُونَ عَلَى اللهِ حَقَّ تَوَكُّلِهِ، لَرَزَقَكُمْ كَمَا يَرْزُقُ الطَّيْرَ، تَغْدُو خِمَاصًا وَتَرُوحُ بِطَانًا».

Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Alah Ya yarda da shi - ya ce: Ya ji Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Da a ce za ku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro, da Ya azurtaku kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace kuma ya yi yammaci a ƙoshe".

Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi Musnad Ahmad - 205

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana kwaɗaitar da mu da cewa mu dogara ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - wajen jawo amfani da tunkuɗe cuta a al'amuran duniya da Addini, domin cewa ba mai bayarwa, ba mai hanawa, ba mai cutarwa, ba mai amfanarwa sai shi - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka-, kuma mu aikata sabubban da za su jawo mana amfani su tunkuɗe mana cuta tare da gaskiyar dogaro ga Allah, a duk lokacin da muka aikata haka Allah Zai azurtamu kamar yadda Yake azurta tsuntsun da yake fita da safe alhali yana a yunwace, sannan ya dawo da yamma alhali cikinsa a cike, wannan aikin daga tsuntsu wani nau'i ne daga sabubba a tafiya don neman arziki, ba tare da ƙaryar dogaro ba da kuma kasala.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar dogaro ga Allah, kuma yana daga mafi girman sabubban da ake jawo arziki da su.
  2. Tawakkali ba ya kore sabubba, domin ya ba da labarin cewa tawakkali na haƙiƙa jijjifi da yammaci a neman arziki ba ya kishiyantarsa.
  3. Himmatuwar shari'a da ayyukan zuciya; domin dogaro aiki ne na zuciya.
  4. Rataya da sabubba kawai tawaya ne a addini, barin sabubba kuma tawaya ne a hankali.

Manufofin Fassarorin

69 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
EL Ελληνικά اليونانية
AK Akan الأكانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
LN Lingala اللينجالا
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو