1. Gida
  2. kashe kashe
  3. SIRA DA TARIHI

Sabuntawa Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«اللهُمَّ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ، فَأَيُّمَا رَجُلٍ مِنَ المُسْلِمِينَ سَبَبْتُهُ أَوْ لَعَنْتُهُ أَوْ جَلَدْتُهُ فَاجْعَلْهَا لَهُ زَكَاةً وَرَحْمَةً».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi».

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 2601

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya yi addu'a sai ya ce: Ya Allah ? Kaɗai ni mutum ne, ina yin fushi kamar yadda ɗan Adam yake yin fushi, duk muminin da na cutar da shi ko na zage shi na aibanta shi, ko na tsine masa na yi masa mummunar addu'a da korewa daga rahamarKa, ko na dake shi da bulala, to ka sanya hakan ya zama tsarkaka da kusanci da tsarkakewa da kaffara da kuma rahamar da zaka yi masa rahama da ita.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girman ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. Ibnu Hajar ya ce: A cikin Hadisin akwai cikar tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kyawawan ɗabi'unsa da karamcin zatinsa, inda ya fuskanci abin da ya afku daga gare shi da gyarawa da kuma girmamawa.
  3. Nawawi ya ce: Idan an ce: Ta yaya zai yi mummunar addu'a akan wanda bai cancanci mummunar addu'a ba ? ko ya zage shi ko ya tsine masa da makamancin hakan? Amsa ita ce abin da malamai suka amsa da shi, a taƙaice ta fuska biyu: Na farkonsu: Abin da ake nufi da wanda bai cancanci hakan ba a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -, haka a cikin baɗinin al'amari, sai dai cewa shi a zahiri ya cancanci hakan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyanar da cancantarsa ga hakan da alamu na shari'a, kuma ya zama a baɗini al'amari bai cancanci hakan ba, kuma shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abin umarta ne da yin hukunci a zahiri, Allah ne Yake jiɓintar sirrika. Na biyu: Cewa abin da ya faru na zaginsa da mummunar addu'arsa da makancinsa to ba abin nufi ba ne, kai shi yana daga abin da al'adar larabawa ta gudana da shi a cikin sadar da zancensu ba tare da niyya ba. Kamar faɗinsa: Damanka ya talauta, da ciwo ya sameka a fata da maƙogwaro, a cikin wannan hadisn: (Kada shekarunka su yi yawa), a cikin hadisin Mu'awiya: Kada Allah Ya ƙosar da cikinka, da makamancin haka, basa nufin wani abu daga haƙiƙanin addu'a, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ji tsoron kada amsa addu'ar ta dace da wani abu daga hakan, sai ya roƙi Ubangijinsa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya kwaɗaitar da ya sanya hakan ya zama rahama da kaffara da kusanci da tsarkakkewa da kuma lada, kaɗai hakan yana bayyana ne daga gare shi a lokaci kaɗan daga cikin zamaninsa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mai alfasha ba, haka ba ya ɗorawa kansa yawan yin alfasha, kuma ba mai yawan tsinuwa ba ne, ba kuma mai ɗaukar fansa ne da kansa ba.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية