1. Gida
  2. kashe kashe
  3. SIRA DA TARIHI

Sabuntawa Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -

عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ نَبِيَّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَتَبَ إِلَى كِسْرَى، وَإِلَى قَيْصَرَ، وَإِلَى النَّجَاشِيِّ، وَإِلَى كُلِّ جَبَّارٍ يَدْعُوهُمْ إِلَى اللهِ تَعَالَى، وَلَيْسَ بِالنَّجَاشِيِّ الَّذِي صَلَّى عَلَيْهِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ.

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, amma ba Najjashin da Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sallah ba.

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 1774

Bayani

Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin rasuwarsa ya yi rubutu zuwa ga waɗanda ke kewaye da shi daga sarakunan al'ummu, yana kiransu zuwa ga Musulunci; sai ya rubuta zuwa ga Kisra, shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Farisawa, haka zuwa ga Ƙaisara shi kuma laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Rum, haka zuwa ga Najjashi shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Habasha. Kuma ya rubuta zuwa ga kowane sarki mai tsaurin kai wanda ya yi wa mutane tumbe, ya rinjaye su, kuma Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bayyana cewa Najjashin da aka rubuta masa ba Najjashin da ya musulunta ba ne kuma ya rasu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa sallah.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin kiran waɗanda ba musulmai ba zuwa Musulunci, wanda ya haɗa manyan sarakunansu da kuma ƙananan sarakuna.
  2. Halaccin yin aiki da littafi da kuma wasiƙu.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية