1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ:
مَا أَكَلَ آلُ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَكْلَتَيْنِ فِي يَوْمٍ إِلَّا إِحْدَاهُمَا تَمْرٌ.

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 6455

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa cin abinci sau biyu ba a rana ɗaya sai ɗayan ya zama dabino ne.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da iyalan gidansa, sauda yawa a rana ɗaya ma basu samun wani abin da zasu ci sai abinci ɗaya.
  2. Dabino ya kasance shine mafi sauƙi a wurinsu akan waninsa.
  3. Falalar gudun duniya da wadatuwa da kaɗan a rayuwa, kuma kasancewarsa yana daga ɗabi'un Annabawa, da kuma tarihin shugaban Manzanni.
  4. Cin abinci sau biyu a rana ɗaya yana daga cikin al'amuran da aka halatta, kuma hakan yana daga cikin sanannun al'adun larabawa, domin sun kasance a rana ɗaya suna ci ne sau biyu, abincin rana da abincin dare.

Manufofin Fassarorin

29 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية