1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«المُسْلِمُ مَنْ سَلِمَ المُسْلِمُونَ مِنْ لِسَانِهِ وَيَدِهِ، وَالمُهَاجِرُ مَنْ هَجَرَ مَا نَهَى اللَّهُ عَنْهُ».

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 10

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi mai cikakken Musulunci shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa ba ya zaginsu kuma ba ya la'antarsu, ba ya gulmarsu, kuma ba ya tafiya tsakaninsu da kowanne nau'i na nau'ukan cutarwa da harshensa, kuma suka kubuta daga hannunsa ba ya yi musu ta'addanci, ba ya ƙwatar dukiyoyinsu ba tare da wani haƙƙi ba, da makamantan hakan, mai hijira shi ne wanda ya bar abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Cikar Musulunci ba ya kasancewa sai da rashin cutar da wasu ta kowanne bangare.
  2. An kebance harshe da hannu da ambato; Dan yawan kura-kuransu da cutarsu, domin mafi girman sharruka suna bijirowa ne daga garesu.
  3. Kwadaitarwa akan barin sabo, da lazimtar abinda - Allah Madaukakin sarki - Ya yi umarni da shi.
  4. Mafificin musulmai shi ne wanda ya sauke haƙƙoƙin Allah - Madaukakin sarki - da haƙƙoƙin musulmai.
  5. Yin ta'addanci yakan kasance da magana ko da aiki.
  6. Cikakkiyar hijira ita ce kauracewa abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.

Manufofin Fassarorin

57 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية