1. Gida
  2. kashe kashe
  3. DA'AWA DA HISBA

Sabuntawa Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa

عَنِ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رَضيَ اللهُ عنها زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
أَنَّ الْحَوْلَاءَ بِنْتَ تُوَيْتِ بْنِ حَبِيبِ بْنِ أَسَدِ بْنِ عَبْدِ الْعُزَّى مَرَّتْ بِهَا وَعِنْدَهَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقُلْتُ: هَذِهِ الْحَوْلَاءُ بِنْتُ تُوَيْتٍ، وَزَعَمُوا أَنَّهَا لَا تَنَامُ اللَّيْلَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَنَامُ اللَّيْلَ! خُذُوا مِنَ الْعَمَلِ مَا تُطِيقُونَ، فَوَاللهِ لَا يَسْأَمُ اللهُ حَتَّى تَسْأَمُوا».

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:
Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce: Wannan Haula'u ce Bnit Tuwait, kuma sun yi da'awar cewa bata baccin dare, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Bata baccin dare! Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa».

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 785

Bayani

Haula'u Bnt Tuwait - Allah Ya yarda da ita - ta kasance a wurin uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo gurinta (Nana A'isha), sai (Haula'u) ta fita ta barta Sai Nana A'isha ta ce masa: Wannan matar bata baccin dare, kai tana raya shi da sallah. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai tsananin yi mata inkari: Bata baccin dare! ku shagalta da aiki na gari wanda zaku iya dawwama a kansa, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa akan baiwa bayinSa salihai masu biyayya lada da sakamako akan biyayyarsu da kuma kyawawan ayyukansu da kuma ayyukansu na gari har sai sun ƙosa sun bar aikin.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Yawaita ibada sama da yadda jiki zai iya, yana kaiwa zuwa ga ƙosawa da kuma yankewa sai zuciya ta daina yin aikin.
  2. Daidaituwa da tsakatsaki a cikin yin ibada hakan yana sawa a ci gaba da ibadar da kuma tabbata a kanta.
  3. Kanƙanin aiki da aka dawwama ana yi ya fi alheri akan aiki mai yawa mai sa a yanke aikin.
  4. Nawawi ya ce: Ta hanyar dawwama da aiki kaɗan ɗa'a tana zarcewa da zikiri da muraƙaba da ikhlasi da kuma fuskanta ga Allah, saɓanin aiki mai yawa mai wahalarwa har aiki ɗan kaɗan ya ƙaru ta inda zai fi mai yawa wanda aka daina da lada mai yawa.

Manufofin Fassarorin

37 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية