1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ قَالَ حِينَ يَسْمَعُ النِّدَاءَ: اللَّهُمَّ رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ، وَالصَّلاَةِ القَائِمَةِ، آتِ مُحَمَّدًا الوَسِيلَةَ وَالفَضِيلَةَ، وَابْعَثْهُ مَقَامًا مَحْمُودًا الَّذِي وَعَدْتَهُ، حَلَّتْ لَهُ شَفَاعَتِي يَوْمَ القِيَامَةِ».

Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama".

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 614

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah bayan ya gama:
(Ya Allah Ma’abocin wannan kiran) sune lafuzan kiran sallah waɗanda ake kira zuwa bautar Allah da kuma sallah da su, (cikakkiya) cikakkiya, kira zuwa ga Tauhidi da saƙo, (da sallar da za'a tayar) dawwamammiya wacce za'a tayar, (Ka bawa) Ka bawa, ((Annabi) Muhammad al-Wasila) matsayi maɗaukaki a cikin aljanna wanda ba ya kamata sai gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, (da Fadila) daraja ce mai ƙaruwa akan darajoji kan halittu, (Ka tashe shi) Ka ba shi (matsayi abin yabo) wanda ake yabon mai tsayawa a cikinsa; shi ne babban ceto a ranar alƙiyama, (wanda Ka yi masa alƙawari) da faɗinKa: {Ana kaunar Ubangijinka ya tasheka a wani matsayi abin yabo} da ya kasance gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Wanda ya yi wannan addu'ar ya cancanci kuma ceton Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajaba a gare shi ranar alƙiyama.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin wannan addu'ar bayan gama maimaita (kiran sallah) a bayan ladan, wanda bai ji kiran sallah ba; to shi ba zai faɗeta ba.
  2. Matsayin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda aka ba shi Wasila da Fadila da matsayi abin yabo da babban veto a kan rabewa tsakanin halittu.
  3. Tabbatar da ceto ga Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; saboda faɗinsa: "Cetona ya halatta gare shi ranar alƙiyama".
  4. Cetonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kasancewa ne ga ma'abota manyan zunubai daga al'ummarsa a cikin rashin shiga wuta ko kuma a fitar da wanda ya shigeta, ko kuma a shiga aljanna ba tare da hisabi ba, ko ɗaukaka darajojin wanda ya shigeta.
  5. AlƊaibi ya ce: Daga farkonsa zuwa faɗinsa: "(Annabi) Muhammad Manzon Allah ne" ita ce cikakkiyar kira, Hai'ala kuma ita ce sallar da za'a tayar a cikin faɗinsa suna tsaida sallah, za'a iya ɗaukar cewa ya zama abin nufi da sallar addu'a da kuma za'a tayar madawwamiya daga ya tsaya akan abu idan ya dawwama a kansa, akan haka ne to faɗinsa: "Da sallah dawwamammiya" bayani ne ga kira cikakke, kuma zai iya ɗaukar cewa ya zama abin nufi da sallar wacce a za’a yi ake kira zuwa gareta a wannan lokacin ita ce mafi bayyana.
  6. AlMuhallab ya ce: A cikin hadisin akwai kwaɗaitarwa akan yin addu'a a lokutan salloli; domin loakaci ne na fatar amsar Addu’a .

Manufofin Fassarorin

49 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية