1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ سَبَّحَ اللهَ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ ثَلَاثًا وَثَلَاثِينَ، وَحَمِدَ اللهَ ثَلَاثًا وَثَلَاثِينَ، وَكَبَّرَ اللهَ ثَلَاثًا وَثَلَاثِينَ، فَتْلِكَ تِسْعَةٌ وَتِسْعُونَ، وَقَالَ: تَمَامَ الْمِائَةِ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ غُفِرَتْ خَطَايَاهُ وَإِنْ كَانَتْ مِثْلَ زَبَدِ الْبَحْرِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 597

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce bayan ƙare sallar farilla:
Sau talatin da uku: "Tsarki ya tabbata ga Allah" (Subhanallah) shi ne tsarkake Allah daga tawaya.
Da kuma talatin da uku: "Godiya ta tabbata ga Allah" (Alhamdulillah) shi ne yabo gareShi da siffofin cika tare da sonSa da girmamaShi.
Da talatin da uku: "Allah ne Mafi girma" (Allahu Akbar) shi ne cewa Allah ne Mafi girma kuma Mafi ɗaukaka daga dukkan komai.
Da cike adadin ɗarin da faɗin: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai. Ma’anarsa: Babu abin bauta da cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi Maɗaukakin Ya keɓanta da cikakken mulki, wanda ya cancanta da Yabo da kambamawa tare da so da girmamawa banda wanda ba shi ba, kuma Shi mai iko ne babu abin da yake gagarar sa.
Wanda ya faɗi hakan an shafe masa kurakuransa kuma an gafarta masa su, ko da sun kasance kwatankwacin farar kunfa ce wacce take saman kogi lokacin da ya kwaranyo.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so yin wannan zikirin bayan sallolin farilla.
  2. Wannan zikirin sababi ne na gafarar zunubai.
  3. Girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - da rahamarSa da gafararSa.
  4. Wannan zikirin sababi ne na gafarar zunubai, abin nufi: Kankare ƙananan zunubai, amma manyan zunuban babu abinda yake kankaresu sai tuba.

Manufofin Fassarorin

56 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية