1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin kai ba za ka yi wata sujjada ga Allah ba, sai Allah Ya ɗaga darajar ka da ita, kuma Ya sarayar da kuskure da ita

عَنْ مَعْدَانَ بْنِ أَبِي طَلْحَةَ الْيَعْمَرِيُّ قَالَ:
لَقِيتُ ثَوْبَانَ مَوْلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقُلْتُ: أَخْبِرْنِي بِعَمَلٍ أَعْمَلُهُ يُدْخِلُنِي اللهُ بِهِ الْجَنَّةَ؟ أَوْ قَالَ قُلْتُ: بِأَحَبِّ الْأَعْمَالِ إِلَى اللهِ، فَسَكَتَ. ثُمَّ سَأَلْتُهُ فَسَكَتَ. ثُمَّ سَأَلْتُهُ الثَّالِثَةَ فَقَالَ: سَأَلْتُ عَنْ ذَلِكَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «عَلَيْكَ بِكَثْرَةِ السُّجُودِ لِلَّهِ، فَإِنَّكَ لَا تَسْجُدُ لِلَّهِ سَجْدَةً، إِلَّا رَفَعَكَ اللهُ بِهَا دَرَجَةً، وَحَطَّ عَنْكَ بِهَا خَطِيئَةً» قَالَ مَعْدَانُ: ثُمَّ لَقِيتُ أَبَا الدَّرْدَاءِ فَسَأَلْتُهُ فَقَالَ لِي: مِثْلَ مَا قَالَ لِي: ثَوْبَانُ.

Daga Ma’adan ɗan Abu Dalha Al-Ya'amury ya ce:
Na gamu da Sauban 'yantaccen bawan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai na ce: Ka ba ni labari da wani aikin da zan aikata shi Allah Ya shigar da ni Aljanna da shi? ko ya ce, na ce: Da mafi son ayyuka zuwa ga Allah, sai ya yi shiru. Sannan na tambaye shi, sai ya yi shiru, sannan na tambaye shi a karo na uku sai ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da wannan, sai ya ce: "Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin kai ba za ka yi wata sujjada ga Allah ba, sai Allah Ya ɗaga darajar ka da ita, kuma Ya sarayar da kuskure da ita" Ma'adan ya ce: Sannan na gamu da Abu al-Darda'i sai na tambaye shi sai ya fada min abinda Sauban ya faɗa mini.

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 488

Bayani

An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikin da zai zama sababin shiga aljanna, ko game da mafi soyuwar ayyuka a wurin Allah?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce wa mai tambayar: Ka lazimci yawan sujjada a cikin sallah, domin kai ba za ka yi wa Allah sujjada ba sai Ya ɗaga darajarka da ita, kuma Ya kankare kurakuranka da ita.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Zaburar da musulmi akan kwaɗayi ga sallah ta farilla da nafila, saboda yadda ta kunshi sujjada.
  2. Bayanin zurfin ilimin sahabbai da saninsu cewa aljanna ba'a samunta - bayan rahamar Allah - sai da aiki.
  3. Sujjada a cikin sallah tana daga mafi girman sabubban ɗaga darajoji, da gafarta zunubai.

Manufofin Fassarorin

57 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية