1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«‌إِنَّ ‌أَثْقَلَ صَلَاةٍ عَلَى الْمُنَافِقِينَ صَلَاةُ الْعِشَاءِ وَصَلَاةُ الْفَجْرِ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِيهِمَا لَأَتَوْهُمَا وَلَوْ حَبْوًا، وَلَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ بِالصَّلَاةِ فَتُقَامَ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلًا فَيُصَلِّيَ بِالنَّاسِ، ثُمَّ أَنْطَلِقَ مَعِي بِرِجَالٍ مَعَهُمْ حُزَمٌ مِنْ حَطَبٍ إِلَى قَوْمٍ لَا يَشْهَدُونَ الصَّلَاةَ، فَأُحَرِّقَ عَلَيْهِمْ بُيُوتَهُمْ بِالنَّارِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 651

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba da labari game da munafukai da kasalarsu a kan zuwa sallah, musamman ma sallar Issha'i da Asuba, kuma cewa su da ace suna sanin girman lada da sakamako a halartarsu tare da jama'ar musulmai da sun zo musu ko da da rarrafe ne kamar rarrafen yaro da hannaye da kuma gwiwoyi.
Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi niyyar ya yi umarni a tsai da Sallah, sai ya sanya wani mutumin ya yi wa mutane limanci a maimakonsa, sannan ya tafi tare da shi akwai wanda zai ɗauki ɗauri na itatuwa zuwa mazajen da ba sa zuwa sallar jama'a, sai ya ƙona gidajensu da wuta; sabo da tsananin abin da suka aikata na laifi a hakan, - sai dai bai aikata ba - sabo da abinda ke cikin gidaje na mata da yara da babu-ruwansu da kuma wasunsu cikin masu uzuri waɗanda ba su da wani laifi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haɗarin ƙin zuwa sallar jam’i a masallaci.
  2. Munafukai ba sa nufin komai a ibadarsu sai riya da jiyarwa, ba sa zuwa sallah sai lokacin da mutane suke ganainsu.
  3. Girman ladan sallar issha'i da Asuba tare da jama'a, kuma cewa su sun cancanci a zo musu ko da da rarrafe ne.
  4. Kiyaye sallar Issha'i da Asuba kubuta ce daga munafunci, kuma ƙin zuwar musu yana daga siffofin maunafukai.

Manufofin Fassarorin

60 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية