1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?

عَنْ سَعْدِ بنِ أبي وَقَّاصٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
كُنَّا عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَيَعْجِزُ أَحَدُكُمْ أَنْ يَكْسِبَ، كُلَّ يَوْمٍ أَلْفَ حَسَنَةٍ؟» فَسَأَلَهُ سَائِلٌ مِنْ جُلَسَائِهِ: كَيْفَ يَكْسِبُ أَحَدُنَا أَلْفَ حَسَنَةٍ؟ قَالَ: «يُسَبِّحُ مِائَةَ تَسْبِيحَةٍ، فَيُكْتَبُ لَهُ أَلْفُ حَسَنَةٍ، أَوْ يُحَطُّ عَنْهُ أَلْفُ خَطِيئَةٍ».

Daga Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya ce
Mun kasance a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: «Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?» Sai wani mai tambaya daga mazauna wajen ya tambaye shi: Ta yaya ɗayammu zai samu kyakykyawan aiki dubu? Ya ce: «Ya yi tasbihi sau ɗari, sai a rubuta masa kyakykyawa dubu, ko kuma a sarayar masa da kura-kurai dubu».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2698

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin ɗayanku zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana? Sai ɗaya daga cikin mazauna a gurinsa ya ce: Ta yaya mutum zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana cikin sauƙi? Ya ce: To ya ce: "Subhanal Lahi". sau ɗari; sai a rubuta masa kaykkyawa dubu; domin cewa kyakkyawa ɗaya da kwatankwacinsa goma ne, ko kuma a kankare masa mummuna dubu daga cikin munanan ayyukansa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan falaloli; domin cewa su ne tsanin ayyukan biyayya.
  2. Falalar tasbihi da zikiri, kuma cewa wannan aikin mai sauƙi ne wanda mutum ba zai ɗorawa kansa komai ba, da shi ne mutum zai samu wannan ladan mai girma.
  3. Gaggawar sahabbai zuwa aikata aikin alheri ba tare da wani jinkiri ba.
  4. Ninka kyawawan ayyuka zuwa kwatankwacinsu sau goma, hakan misalin faɗinSa ne - Allah Maɗaukakin sarki -: (Wanda ya zo da kyakkyawa to yana da kwatankwacinsa goma) [Al-An'am: 160], wannan shi ne mafi ƙarancin matakan ninkawa, inba haka ba ai tabbas haƙiƙa ya zo zuwa ninki ɗari bakwai.
  5. Ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi canjin (Au (ko)) (Wa (da)) a cikin faɗinsa: Ko a sarayar masa... Al-Ƙari ya ce: Wau takan zo da ma'anar Au, dan haka babu saɓani tsakanin ruwayoyi biyun, kamar ma'ana: Cewa wanda ya faɗeta za'a rubuta masa kyakkyawa dubu, idan bai zamo a kansa ba sai a sarayar masa da wani abu a kuma ba shi wani abu, kuma zai iya yi wuwa Au ɗin ta kasance da ma'anar Wau, ko da ma'anar kai, to a wannan lokacin sai a haɗa tsakaninsu, kuma falalar Allah ta fi yalwa daga hakan ya ƙare, cewa shi za'a rubuta masa kyawawan lada dubu kuma a sarayar masa da munanan ayyuka dubu.

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية