1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai

عَن عبدِ اللهِ بن خُبَيب رضي الله عنه أنه قال:
خَرَجْنَا فِي لَيْلَةٍ مَطِيرَةٍ وَظُلْمَةٍ شَدِيدَةٍ، نَطْلُبُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؛ يُصَلِّي لَنَا، قَالَ: فَأَدْرَكْتُهُ، فَقَالَ: «قُلْ»، فَلَمْ أَقُلْ شَيْئًا، ثُمَّ قَالَ: «قُلْ»، فَلَمْ أَقُلْ شَيْئًا، قَالَ: «قُلْ»، فَقُلْتُ: مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «{قُلْ هُوَ اللهُ أَحَدٌ} وَالْمُعَوِّذَتَيْنِ حِينَ تُمْسِي وَتُصْبِحُ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، تَكْفِيكَ مِنْ كُلِّ شَيْءٍ».

Daga Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce:
Mun fita cikin dare da akai ruwa da duhu mai tsanani, muna neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallah, ya ce: Sai na riske shi, sai ya ce: "Ka ce", ban cekomai ba, sannan ya ce: "Ka ce", ban ce komai ba, sai ya ce: "Ka ce" sai na ce: Me zan ce? Ya ce: Ka ce: "{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai".

Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi Sunan Tirmizi - 3575

Bayani

Sahabi mai girma Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin: Cewa sun fita a dare mai yawan ruwa, kuma duhu ya kasance mai tsanani dan neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; Domin ya yi musu sallah, sai suka same shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka ce" wato ka karanta, bai karanta komai ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake fada masa, sai Abdullahi ya ce: Mezan karanta ya Manzon Allah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka karanta Surat Al-Ikhlas {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai}, da Falaki da Nasi {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina nemn tsari da Ubangijin mutane}, a lokacin yammaci, da lokacin safiya, sau uku za su kiyayeka daga kowanne sharri, kuma zasu kareka daga kowanne mummunan abu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so karanta Suratul Al-ikhlas da Falaki da Nasi safe da yamma, kuma su tsari ne daga kowanne sharri.
  2. Falalar karanta Suratul Al-Ikhlas da Falaki da Nasi.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية