1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«الْإِيمَانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ -أَوْ بِضْعٌ وَسِتُّونَ- شُعْبَةً، فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الْأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنَ الْإِيمَانِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 35

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewar imani rassa ne, kuma halaye ne masu yawa, sun kunshi ayyuka da ƙudurce-ƙudurcen zuciya da maganganu.
Kuma mafi girman ɗabi’un imani da falala shi ne faɗin: "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah". Tare da sanin ma’anarta, da kuma aiki da abin da take nunawa na cewa Allah Shi ne abin bauta guda ɗaya, wanda Ya cancanci a bauta masa Shi kaɗai ban da wani ba shi ba.
Kuma mafi ƙarancin ayyukan imani shi ne kawar da duk abin da zai cutar da mutane a kan hanyoyi.
Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin cewa kunya tana cikin ɗabi’u na imani, kuma ɗabi’a ce da take zaburarwa a kan yin abu mai kyau da kuma barin mummuna.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Imani matakai ne, wani sashin nasu ya fi wani falala.
  2. Imani kuma magana ce da kuma aiki da ƙudurin zuci
  3. Jin kunyar Allah maɗaukaki yana sanyawa kada ya ganka a inda ya hanaka, kada kuma ya rasaka a inda ya umarceka.
  4. Anbaton adadi ba ya nuna iyakarsu kenan, sai dai yana nuna yawan ayyukan imani ne, domin Larabawa su kan ambaci abu da adadi ba tare da suna nufin kore abin da ba shi ba.

Manufofin Fassarorin

63 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية