1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«إِذَا مَاتَ الْإِنْسَانُ انْقَطَعَ عَنْهُ عَمَلُهُ إِلَّا مِنْ ثَلَاثَةٍ: إِلَّا مِنْ صَدَقَةٍ جَارِيَةٍ، أَوْ عِلْمٍ يُنْتَفَعُ بِهِ، أَوْ وَلَدٍ صَالِحٍ يَدْعُو لَهُ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 1631

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa aikin mamaci yana yankewa da rasuwarsa,, kyawawan ayyuka basa samunsa bayan mutuwnrsa sai a waɗannan ukun; dan kasancewarsa ya zama sababinsu:
Na farko: Sadakar da ladanta yake gudana kuma yake dawwama, ba mai yankewa ba, kamar waƙafi, da gina masallatai, da haƙa rijiyoyi, da wanin hakan.
Na biyu: Ilimin da mutane suke anfanuwa da shi, kamar wallafa littattafan ilimi, ko kamar ya koyar da wani mutum, sai wannan mutumin ya yaɗa wannan ilimin bayan mutuwarsa.
Na uku: Ɗa na gari mumini da zai yi masa addu'a.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ma'abota ilimi sun haɗu akan cewa daga abinda yake riskar mutum bayan mutuwarsa na lada: Sadaka mai gudana, da ilimin da ake anfanuwa da shi, da addu'a, kuma ya zo a cikin wasu Hadisan daban: Hajji kuma.
  2. An keɓanci waɗannan ukun da ambato a cikin wannan Hadisin; domin sune tushen alheri, kuma mafi rinjayar abinda ma'abota falala suke nufin wanzuwarsa bayansu.
  3. Dukkan ilimin da ake anfanuwa da shi to shi lada yana samuwa gare shi, sai dai ƙololuwarsu shi ne ilimi na shari'a da ilimummuka masu ƙarfafarsa.
  4. Ilimi mafi anfani shi ne waɗannan ukun; domin ilimi mutumin da yake neman saninsa yana anfanuwa da shi, akwai kiyaye shari'a a cikin ilimi, akwai anfanar halitta a gamewa, shi ne mafi ƙunsa kuma mafi gamewa; domin shi yana neman iliminka samamme a cikin rayuwarka kuma samamme bayan mutuwarka.
  5. Kwaɗaitarwa akan tarbiyyar yara salihai; su ne waɗanda suke anfanar iyayensu a lahira, daga anfanar su suna yi musu addu'a.
  6. Kwaɗaitarwa akan kyautatawa mahaifa bayan mutuwarsu, shima yana daga aikin alherin ɗa zai anfana da shi.
  7. Addu'a tana anfanar mamaci koda daga wanin ɗa ne, sai dai ankeɓanci ɗa da ambato; domin shi ne wanda yake ci gaba a addu'a ga mutum a galibi har zuwa mutuwarsa.

Manufofin Fassarorin

51 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية