1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت:
دَخَلَتْ هِنْدٌ بِنْتُ عُتْبَةَ امْرَأَةُ أَبِي سُفْيَانَ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَتْ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ أَبَا سُفْيَانَ رَجُلٌ شَحِيحٌ، لَا يُعْطِينِي مِنَ النَّفَقَةِ مَا يَكْفِينِي وَيَكْفِي بَنِيَّ إِلَّا مَا أَخَذْتُ مِنْ مَالِهِ بِغَيْرِ عِلْمِهِ، فَهَلْ عَلَيَّ فِي ذَلِكَ مِنْ جُنَاحٍ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خُذِي مِنْ مَالِهِ بِالْمَعْرُوفِ مَا يَكْفِيكِ وَيَكْفِي بَنِيكِ».

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Hindu 'yar Utbatah - matar Abu Sufyan- ta shigo wajen Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ta ce: Ya Manzon Allah, Abu Sufyan ya kasance mutum ne mai ƙwauro, ba ya bamu abin da zai ishe mu ni da 'ya'ya na sai abinda na ɗauka daga cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba, shin ba laifi akaina a yin hakan? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 1714

Bayani

Hindu 'yar Utbah - Allah Ya yarda da ita - ta nemi fatawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mijinta Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi -, kuma shi mutum ne marowaci mai kwaɗayin dukiyarsa, ba ya bata abinda zai isheta ya ishi 'ya'yanta na ciyarwa, sai dai in ta ɗauka a ɓoye cikin dukiyarsa alhali shi bai sani ba, shin akwai wani laifi akanta a hakan? Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ki ɗauki gwargwadan abinda aka sani a al'ada cewa shi zai isa cikin dukiyarsa koda ba tare da saninsa ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin ciyar da mata da kuma 'ya'ya.
  2. Ibnu Hajar ya ce: Abin nufi a faɗinsa: "Ki ɗauki abinda zai isheki cikin dukiyarsa ta yadda al'ada take gudana da shi", sai ya mayar da ita zuwa ga al'ada a cikin abinda babu iyakancewar shari'a a cikinsa.
  3. Ibnu Hajar ya ce: An kafa hujja da wanna hadisin akan halaccin ambatan mutum da abinda ba ya ƙayatar da shi idan ya kasance ta fuskar neman fatawa ne da kai ƙara da makamancin haka, kuma shi ne ɗaya daga cikin guraren da aka halatta giba (yi da mutum) a cikinsu.
  4. AlƘurɗubi ya ce: Hindu bata nufin siffanta Abu Sufyan da ƙwauro a dukkanin halayensa, kawai ta siffanta halinta ne tare da shi kuma cewa shi yana yi mata ƙwauro ita da 'ya'yanta, wannan ba ya lazimtar rowa kai tsaye, domin cewa mafi yawancin shugabanni sunayin haka tare da iyalansu suna fifita na waje dan jawo zukatansu.

Manufofin Fassarorin

40 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية