1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye (‘yanta baiwa), da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; to mafi girman su a lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قالَ: قالَ رَسُولُ اللَّهِ صلَّى اللَّهُ عليْه وسلَّمَ:
«دِينَارٌ أَنْفَقْتَهُ فِي سَبِيلِ اللهِ، وَدِينَارٌ أَنْفَقْتَهُ فِي رَقَبَةٍ، وَدِينَارٌ تَصَدَّقْتَ بِهِ عَلَى مِسْكِينٍ، وَدِينَارٌ أَنْفَقْتَهُ عَلَى أَهْلِكَ أَعْظَمُهَا أَجْرًا الَّذِي أَنْفَقْتَهُ عَلَى أَهْلِكَ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye (‘yanta baiwa), da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; to mafi girman su a lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 995

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci sashin nau’ukan ciyarwa, sai ya ce: Dinarin da ka ciyar da shi a yaƙi a tafarkin Allah, da dinarin da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye da bauta, da dinarin da ka yi sadaka ga miskini mabuƙaci, da dinarin da ka ciyar da shi ga iyalanka, sannan ya bada labarin cewa mafi girmansu a lada a wajen Allah shi ne wanda ka ciyar da shi ga iyalanka da wanda ciyar da shi ya lazimceka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Yawan ƙofofin ciyarwa a tafarkin Allah.
  2. Gabatar da abin da ya fi a cikin babin ciyarwa a lokacin cinkoso, yana daga hakan ciyarwa ga iyali a lokacin da ciyarwa ga gabaɗayan ba zai yi wu ba.
  3. Nawawi ya faɗa a Sharhin Muslim: Kwaɗaitarwa akan ciyarwa ga iyalai, da kuma bayanin girman lada a cikinta; domin daga cikinsu akwai wanda ciyarwarsa take wajaba ta hanyar kusanci, daga cikinsu akwai wanda take zama mustahabbi kuma tana zama sadaka da sada zumunci, kuma daga cikinsu akwai wadda take zama wajiba ta hanyar mallakar aure ko mallakar dama (bayi), wannan dukkansa mai falala ne kuma abin kwaɗaitarwa ne a kansa, kuma shi ya fi sadakar nafila.
  4. Sindi ya ce: Faɗinsa: (Dinaren da yake ciyar da shi ga iyalansa), wato: Idan ya yi hakan don Allah kuma ya yi nufin haƙƙin iyalai misali.
  5. Abu Kilaba ya ce; Wane mutum ne mafi girman lada daga mutumin da yake ciyarwa ga iyalai ƙanana da zai karesu ko Allah Ya anfanar da su da shi kuma ya wadata su?!

Manufofin Fassarorin

43 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية