1. Gida
  2. kashe kashe
  3. SIRA DA TARIHI

Sabuntawa Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -

عَنِ الْبَرَاءِ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
مَا رَأَيْتُ مِنْ ذِي لِمَّةٍ أَحْسَنَ فِي حُلَّةٍ حَمْرَاءَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، شَعْرُهُ يَضْرِبُ مَنْكِبَيْهِ، بَعِيدَ مَا بَيْنَ الْمَنْكِبَيْنِ، لَيْسَ بِالطَّوِيلِ وَلَا بِالْقَصِيرِ.

Daga Bara’u - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - gashinsa yana taɓa kafaɗunsa, mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, shi ba dogo ba ne ba kuma gajere ba ne.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 2337

Bayani

Bara’u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi bai taɓa ganin wani mai gashi ba, wanda gashin kansa mai tsawo ne ya kai kafaɗu, kuma yana sanya mayafi da kwarjalle baƙaƙe alhali a cikinsa akwai zanen ja mafi kyau kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -, ya kasance daga cikin siffofinsa na halitta shi mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, mai yalwar ƙirji, kuma ya kasance mai tsakatsakiyar daidaituwa tsakanin tsawo da gajarta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin wasu daga cikin siffofin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - masu kyau a zahiri na kyawun gashi da faɗin ƙirji, da kyawun daidaituwa, da makamancin haka.
  2. Son sahabbai masu girma - Allah Ya yarda da su - ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, har cewa su suna hakaitowa kuma suna ruwaito ɗabi'unsa da siffofinsa na jiki da kuma na ma'ana ga na bayansu.

Manufofin Fassarorin

37 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية