1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«السَّاعِي عَلَى الأَرْمَلَةِ وَالمِسْكِينِ، كَالْمُجَاهِدِ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، أَوِ القَائِمِ اللَّيْلَ الصَّائِمِ النَّهَارَ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 5661

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake tsayuwa akan al’amuran matar da mijinta ya rasu alhali ba ta da wani wanda zai tsaya akan lamuran ta, da kuma miskini mabukaci, yana ciyar dasu yana mai neman lada a wurin Allah - Madaukakin sarki -, to shi a lada kamar mayakine a tafarkin Allah, ko kamar mai tsayuwa ne a sallar tahajjudin da baya gajiya, mai azimin da ba ya hutawa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa akan taimamkekeniya da toshe bukatun masu rauni.
  2. Ibada ta kunshi kowane aiki na gari, daga ibada akwai kaikawo ga wacce mijinta ya rasu da kuma miskini.
  3. Dan Hubaira ya ce: Abin nufi cewa Allah - Madaukakin sarki - Zai tattaro masa ladan mai azimi da mai tsayuwar (dare) alokaci daya; saboda shi ya tsaya ga matar da mijinta ya rasu a matsayin mijinta..., ya kuma tsaya ga miskinin da ya gajiya daga tsayuwa akan kansa, sai ya ciyar da wannan ragowar abincinsa, ya kuma yi sadaka da karfinsa, sai amfaninsa ya zama ya yi daidai da azimi da tsayuwar dare da kuma yaki.

Manufofin Fassarorin

59 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية