1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka guje wa kuturu kamar yadda kake guje wa zaki

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لاَ عَدْوَى وَلاَ طِيَرَةَ، وَلاَ هَامَةَ وَلاَ صَفَرَ، وَفِرَّ مِنَ المَجْذُومِ كَمَا تَفِرُّ مِنَ الأَسَدِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka guje wa kuturu kamar yadda kake guje wa zaki".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 5707

Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin al'amuran Jahiliyya (maguzawa) dan gargaɗi daga gare su, da kuma bayanin al'amari yana hannun Allah, kuma wani abu ba ya kasancewa sai da umarninSa da ƙaddarawarSa, su ne:
Na farko: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna zatan cewa cuta tana yaɗuwa da kanta; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga ƙudirce tashin cuta daga mara lafiya zuwa ga mai lafiya da ɗabi'arta; Allah Shi ne Mai tasarrufi a cikin kasantattu; kuma Shi ne wanda Yake saukar da cuta kuma Yake ɗauketa, hakan ba ya faruwa saida nufinSa da ƙaddarawarSa.
Na biyu: Mutanen Jahiliyya sun kasance idan sun fita dan wata tafiya ko kasuwanci, sai su yi wa tsuntsu tsawa, idan ya tashi ɓangaren dama sai su yi murna, idan ya tashi ɓangaren hagu sai su canfa su dawo, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga wannan canfin da tsuntsu, ya kuma bayyana cewa hakan akida ce ɓatacciya.
Na uku: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna cewa: Idan mujiya ta faɗo a kan wani gida sai musiba ta samu mutanen wannan gidan; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani game da canfa hakan.
Na huɗu: Ya yi hani daga canfa watan Safar, shi ne wata na biyu daga watannin ƙamariyya. (Wasu kuma) suka ce Safar shi ne: Wata micijiya ce da take a ciki tana samun dabbobi da mutane, suna riya cewa ita ce mafi tsananin yaɗuwa daga cutar kirci; sai ya kore wannan akidar.
Na biyar: Ya yi umarni da nisantar wanda aka shafa da cutar kuturta kamar yadda zaka nisanci zaki, hakan dan bai wa kai kariya da kuma nema masa kuɓuta da kuma aikata sabubban da Allah ya yi umarni da su. Kuturta: Wata cuta ce da gaɓɓan mutum suke cin juna daga gareta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin tawakkali ga Allah da dogaro gareShi, da aikata sabubban da aka shara'anta.
  2. Wajabcin imani da hukuncin Allah da ƙaddararSa, kuma sabubba suna hannun Allah, Shi ne wanda Yake gudanar da su ko yake zare tasirinsu.
  3. Bata abinda sashin mutane suke aikatawa na canfi da launuka, kamar baƙaƙe da jajaye, ko sashin lambobi da sunaye da mutane da masu larura.
  4. Akan hani daga kusantar kuturu da makamancinsa masu cututtuka da suke yaɗuwa (da izinin Allah): Hakan yana daga sabubban da Allah Ya gudanar da al'ada cewa su suna kaiwa zuwa ga abinda ya sabbabasu; sabubba ba sa tsayuwa da kansu, kadai Allah Shi ne wanda idan Ya so zai zaresu ba za su tasirantar da komai ba, idan kuma Ya so sai Ya wanzar da su sai su yi tasiri.

Manufofin Fassarorin

57 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية