1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa

عَنْ صَفْوَانَ بْنِ مُحْرِزٍ قَالَ: قَالَ رَجُلٌ لِابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما كَيْفَ سَمِعْتَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: فِي النَّجْوَى؟ قَالَ: سَمِعْتُهُ يَقُولُ:
«يُدْنَى الْمُؤْمِنُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ رَبِّهِ عَزَّ وَجَلَّ، حَتَّى يَضَعَ عَلَيْهِ كَنَفَهُ، فَيُقَرِّرُهُ بِذُنُوبِهِ، فَيَقُولُ: هَلْ تَعْرِفُ؟ فَيَقُولُ: أَيْ رَبِّ أَعْرِفُ، قَالَ: فَإِنِّي قَدْ سَتَرْتُهَا عَلَيْكَ فِي الدُّنْيَا، وَإِنِّي أَغْفِرُهَا لَكَ الْيَوْمَ، فَيُعْطَى صَحِيفَةَ حَسَنَاتِهِ، وَأَمَّا الْكُفَّارُ وَالْمُنَافِقُونَ، فَيُنَادَى بِهِمْ عَلَى رؤُوسِ الْخَلَائِقِ هَؤُلَاءِ الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَى اللهِ».

Daga Safwan ɗan Muhriz ya ce: Wani mutum ya ce wa Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - yaya ka ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: A (sha'anin) sirri? ya ce: Na ji shi yana cewa:
"Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa, sai Ya ce: Shin kana sane ? sai ya ce: Eh ya Ubangiji ina sani, ya ce: Lallai cewa Ni haƙiƙa Na suturtasu gareka a duniya, kuma cewa lallai Ni Zan gafarta maka su a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa, amma kafirai da munafukai, sai a kirasu akan kawunan halittu waɗannan sune waɗanda suka yi wa Allah ƙarya".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 2768

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ganawar Allah ga bawanSa mumini ranar alƙiyama, sai ya ce:
Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa sai Ya sanya suturarSa daga ma'abota wurin tsayuwa har ya zama waninsa ba zai yi tsinkaye akan sirrinsa ba, sai ya ce masa:
Shin kana sanin zunubi kaza da kaza... Zai tabbatar masa da zunuban da suke tsakanin bawa da UbangijinSa.
Sai ya ce: Na'am Eh, ya Ubangiji.
Har idan mumini ya firgita ya ji tsoro, sai Tsarki ya tabbatar maSa Ya ce masa: Lallai cewa Ni na suturta su gareka a duniya, kuma cewa Ni na gafartasu gareka a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa.
Amma kafiri da munafuki sai a yi kira a gabn mahalarta: Waɗannan sune waɗanda suka yi wa Ubangijinsu ƙarya, ku saurara tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar Allah da rahamarSa ga muminai saboda rufa musu asiri a duniya da lahira.
  2. Kwaɗaitarwa akan rufawa mumini asiri gwargwadan iko.
  3. Ayyukan bayi gaba ɗayansu Ubangijin bayi Zai kiyayesu, wanda ya samu alheri to ya godewa Allah, wanda ya samu wanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa, kuma shi yana ƙarƙashin Mashi'ar Allah.
  4. Ibnu Hajar ya ce: Dukkan hadisan sun yi nuni akan cewa masu saɓo cikin muminai a alƙiyama sun kasu gida biyu: Na ɗayansu: Wanda saɓonsa tsakaninsa da Ubanginjinsa ne, sai hadisin Ibnu Umar ya yi nuni akan cewa wannan ɓangaren ya kasu gida biyu: Wani ɓangaren: Saɓonsu zai zama abin suturtawa a duniya, to wannan wanda Allah Zai yi masa sutura ne a alƙiyama shi a mafurtar (hadisn). Wani ɓangaren kuma: Saɓonsu zai zama a bayyane, sai mafhum ɗin sa ya yi nuni akan cewa shi saɓanin haka ne. Bangare na biyu: Wanda saɓonsa tsakanin sa da bayi ne to su sun kasu kashi biyu kuma: Wani ɓangaren: Mummunan ayyukansu sun rinjayi kyawan ayyukansu, to wadannan zasu fada cikin wuta sannan su fita da ceto, wani bangaren kuma: Munanan ayyukansu zasu yi daidai da kyawawan ayyukansu, to wadannan ba zasu shiga aljanna ba har sai sakayya ta faru tsakaninsu.

Manufofin Fassarorin

49 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية