1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ، مَنْ ضَارَّ ضَرَّهُ اللَّهُ، وَمَنْ شَاقَّ شَقَّ اللَّهُ عَلَيْهِ».

Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa".

Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi Sunan Al-DarAl-Kutni - 3079

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, baya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida.
Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta sai dai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana narko da faruwar cuta ga wanda yake cutar da mutane, da kuma faruwar wahala ga wanda yake tsanantawa mutane.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani game da ramuwa da sama da abin da aka yi.
  2. Allah bai umarci bayainsa da wani abu da zai cutar da su ba.
  3. Haramta cuta da cutarwa ta magana ko da aiki ko da bari.
  4. Sakamako yana kasancewa daga jinsin aiki, wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cuta, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawa.
  5. Daga ƙa'idojin shari'a akwai: "Cuta ana gusar da ita", shari'a ba ta tabbatar da cuta, kuma tana inkarin cutarwa.

Manufofin Fassarorin

68 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
EL Ελληνικά اليونانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
LN Lingala اللينجالا
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو