1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, da kun san abinda na sani da kun yi dariya kaɗan kuma kun yi kuka da yawa

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: بَلَغَ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم ‌عَنْ ‌أَصْحَابِهِ ‌شَيْءٌ، فَخَطَبَ فَقَالَ:
«عُرِضَتْ عَلَيَّ الْجَنَّةُ وَالنَّارُ فَلَمْ أَرَ كَالْيَوْمِ فِي الْخَيْرِ وَالشَّرِّ، وَلَوْ تَعْلَمُونَ مَا أَعْلَمُ لَضَحِكْتُمْ قَلِيلًا وَلَبَكَيْتُمْ كَثِيرًا» قَالَ: فَمَا أَتَى عَلَى أَصْحَابِ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَوْمٌ أَشَدُّ مِنْهُ، قَالَ: غَطَّوْا رُءُوسَهُمْ وَلَهُمْ خَنِينٌ، قَالَ: فَقَامَ عُمَرُ فَقَالَ: رَضِينَا بِاللهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ نَبِيًّا، قَالَ: فَقَامَ ذَاكَ الرَّجُلُ فَقَالَ: مَنْ أَبِي؟ قَالَ: «أَبُوكَ فُلَانٌ»، فَنَزَلَتْ: {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَسْأَلُوا عَنْ أَشْيَاءَ إِنْ تُبْدَ لَكُمْ تَسُؤْكُمْ} [المائدة: 101].

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani abu ya kai ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sahabbansa, sai ya yi huɗuba ya ce:
"An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, da kun san abinda na sani da kun yi dariya kaɗan kuma kun yi kuka da yawa" ya ce: Babu wani yini da ya taɓa zowa sahabban manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi tsanani kamar wannan yinin, ya ce: Sai suka rufe kawunansu suna ruri, ya ce: Sai Umar ya miƙe sai ya ce: Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi, ya ce: Sai wani mutum ya miƙe sai ya ce: Waye babana? ya ce: "Babanka shi ne wane", sai wannan ayar ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku tambayi wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Ma'ida: 101].

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 2359

Bayani

Wani abu ya kai ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sahabbansa, cewa su sun yawaita masa tambaya, sai ya yi fushi ya yi huɗuba sai ya ce: An bijiron da aljanna da wuta; ban taɓa ganin mafi alheri a cikin aljanna daga abinda na gan shi a yau ba. Haka (bantaɓa ganin) mafi sharri mafi yawa daga abinda na gan shi a cikin wuta a yau ba, da kun ga abinda na gani, kuma kun san abinda na sani daga abinda na gan shi a yau da kafin yau da kun ji tsoro, tsoro mai yawa, da dariyarku ta ƙaranta, kuma kukanku ya yawaita. Anas - Allah Ya yarda da shi -: Wani yini bai taɓa zo wa sahabbansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - mafi tsanani daga wannan yinin ba, sai suka rufe kawunansu alhali gunji na kuka yana fita daga hanci saboda tsananin kuka. Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya miƙe sai ya ce: "Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi". Ya ce: Sai wancan mutumin ya miƙe, sai ya ce: Waye babana?
Ya ce: "Babanka shi ne wane". sai (aya) ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku yi tambaya game da wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Maa'ida: 101].

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so yin kuka dan tsoron uƙubar Allah, da rashin yawaita dariya; domin cewa dariya tana nuni akan rafkana da bushewar zuciya.
  2. Tasirantuwar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da wa'azin, da tsananin tsoronsu daga uƙubar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  3. An so rufe fuska a lokacin kuka.
  4. AlKhaɗɗabi ya ce: Wannan hadisin ga wanda ya yi tambaya ne dan ɗorawa kai da kuma ta'annuiti a cikin abinda babu buƙatuwa zuwa gare shi, amma wanda ya yi tambaya dan wata larura shi ne cewa wata mas'ala ta faru gare shi sai ya yi tambaya game da ita to babu laifi ko zargi a kansa.
  5. Kwaɗaitarwa akan daidaituwa akan biyayya ga Allah, da nisanta daga saɓon Allah, da tsayuwa a iyakokin Allah.
  6. A cikinsa akwai halaccin yin fushi a lokacin wa'azi da kuma koyarwa.

Manufofin Fassarorin

40 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية