1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا أَتَى الْمَرِيضَ يَدْعُو لَهُ قَالَ: «أَذْهِبِ الْبَاسَ، رَبَّ النَّاسِ، وَاشْفِ أَنْتَ الشَّافِي، لَا شِفَاءَ إِلَّا شِفَاؤُكَ، شِفَاءً لَا يُغَادِرُ سَقَمًا».

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wajan mara lafiya yana yi masa addu'a zai ce : «Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara».

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 2191

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ziyarci wani mara lafiya zai yi masa addu'a sai ya ce: Ya Allah (Ka tafiyar) Ka gusar da (tsanani) da tsananin rashin lafiya, (ya Ubangijin mutane) kuma Mahaliccinsu kuma Mai renansu, (Ka warkar da) wannan mara lafiyar (Kai ne) tsarki ya tabbatar maKa (Mai warkarwa) ina kamun ƙafa zuwa gareKa da sunanKa Mai warkarwa, (babu wata waraka) mai tabbata ga mara lafiya (sai warakarKa) da kuma lafiyarKa, (waraka) kai tsaye (wacce bata bari) ta wanzar ta kuma bar (wata masassara) da wani rashin lafiyar daban.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mai warkarwa Shi ne Allah - Mai girma da ɗaukaka -, amma likita da magani to su biyun sabubba ne basa anfanarwa kuma ba sa cutarwa sai da izinin Allah.
  2. Gaida mara lafiya yana daga haƙƙoƙi tsakanin musulmai, hakan cancanta ga iyalai.
  3. Kwaɗaitarwa ga wanda ya ziyarci mara lafiya ya yi masa wannan addu'ar mai albarka waccea aka ruwaito.
  4. Daga shiryrwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yin magani da ruƙya ta shari'a da Alƙur'ani da kuma addu'o'i masu tsarki, saboda haka tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana yi wa kansa ruƙya idan ya yi rashin lafiya, haka nan yana yi wa wanda ya yi rashin lafiya daga iyalansa da wasunsu ruƙiyya.
  5. Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa yi wa mara lafiya addu'ar waraka tare da abinda ke cikin rashin lafiya na kankare zunubai da lada kamar yadda hadisai suka zo da hakan ya rikitar, to amsa ita ce: Lallai addu'a ibada ce, kuma bata kore lada da kuma kaffara; domin cewa su suna samuwane a farkon rashin lafiyar da kuma haƙuri a kanta, mai addu'a yana tsakanin kyawawa biyu: Kodai abin nufinsa ya samu, ko kuma a canja masa da jawo wani anfanin ko tunkuɗe cuta, kowanne daga cikinsu daga falalar Allah ne.

Manufofin Fassarorin

44 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية