1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin

عَنْ مُعَاذٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمَّا وَجَّهَهُ إِلَى الْيَمَنِ أَمَرَهُ أَنْ يَأْخُذَ مِنَ الْبَقَرِ مِنْ كُلِّ ثَلَاثِينَ تَبِيعًا أَوْ تَبِيعَةً، وَمِنْ كُلِّ أَرْبَعِينَ مُسِنَّةً، وَمِنْ كُلِّ حَالِمٍ -يَعْنِي مُحْتَلِمًا- دِينَارًا أَوْ عَدْلَهُ مِنَ المَعَافِرِ، ثِيَابٌ تَكُونُ بِالْيَمَنِ.

Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi -:
Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika shi zuwa Yaman sai ya umarce shi ya karɓi Tabi'i namiji ko mace (wanda yake bin uwarsa kiwo) daga dukkan (shanu) talatin, haka (ya karɓi) Musinnah daga dukkanin (shanu) arba'in, daga (ya karɓi) dinari ɗaya ko kwatankwacinsa na Ma'afir wasu tufa ne na Yaman daga duk wanda ya isa mafarki.

Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi Sunan Abi Dawud - 1576

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika Mu'az ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi - zuwa Yaman dan koyar da mutane da kuma kiransu, daga cikin abin da ya umarce shi da shi shine ya karɓi Zakkar shanunsu tabi'i ɗaya namiji ko mace daga dukkanin talatin; shine wanda ya cika shekara ɗaya, haka (ya karɓi) Musinna daga dukkanin arba'in; ita ce wacce ta cika shekara biyu. Kuma ya karɓi jizyar dinari ɗaya daga mazowa littafi Yahudawa da Nasara daga dukkanin namiji baligi, ko abin da ya yi daidai da dinari ɗaya na tufafin Yaman waɗanda ake kiransu da: Ma'afirri.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ba'a karɓar jizya sai daga wanda ya isa mafarki; domin cewa ƙa'idar wanda ba'a karɓa daga gare shi ita ce: Shine wanda ba ya halatta a kashe shi idan an ribace shi: Daga ƙaramin yaro, da mace, da wasunsu.
  2. Ƙimanta jizyar yana komawa ne ga ijtihadin liman, domin ita tana saɓawa gwargwadan saɓawar guri da kuma zamani, da wadata da kuma talauci, dalili akan haka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne wanda ya ƙaddara gwargwadanta ga mutanen Yaman, sai ya ce wa Mu'az; "Ka karɓi dinari ɗaya daga dukkanin wanda ya isa mafarki" yayin da jizya ta ƙaru lokacin Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ƙayyade gwargwadanta ga mutanen Sham.
  3. Himmatuwa da tara Zakkah, da kuma wakilta wanda zai tattarota yana daga cikin muhimman ayyukan shugaba.
  4. Tabi'i: Shi ne wanda ya cika shekara ɗaya, ya shiga cikin shekara ta biyu, kuma an ambace shi tabi'i ne; domin shi bai gushe ba yana bin uwarsa kiwo.
  5. Dinari: Kuɗi ne na zinari, dinari na Musulunci: Awonsa shine Gram huɗu da rubu'in zinari (4.25GM).

Manufofin Fassarorin

31 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية