1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku

عن أنس رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«جَاهِدُوا المشركين بأموالكم وأنفسكم وألسنتكم».

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku".

Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shi Sunan Abi Dawud - 2504

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yaƙar kafirai, da yin ƙoƙari a fuskantarsu ta kowace hanya gwargwadan iko dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya, daga hakan:
Na farko: Ciyar da dukiya a yaƙarsu; na siyan makamai da ciyarwa ga mayaƙa da makamancin hakan.
Na biyu: Fita da rai da jiki dan haɗuwa da su da kuma tunkuɗesu.
Na uku: Da kiransu ga wannan Addinin da harshe, da tsaida hujja akansu, da tsawatar da su da yi musu raddi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan yaƙar mushrikai da rai da dukiya da kuma harshe; kowa gwargwadan ikonsa, kuma yaƙi ba ya taƙaituwa akan yaki da rai kadai.
  2. Umarni da yaƙi na wajabci ne, zai iya zama wajibi aini (akan kowa da kowa), kuma zai iya zama wajibi kifa'i (wasu sun ɗaukewa wasu).
  3. Allah Ya shar’anta jihadi saboda wasu al'amura daga cikinsu: Na farko: Faɗa da shirka da mushrikai; domin cewa Allah ba Ya karɓar shirka har abada. Na biyu: Kawar da wahalhalun da suke bijirowa hanyar kira zuwa ga Allah. Na uku: Kiyaye aƙida daga dukkan abinda yake kishiyantarta. Na huɗu: Kariya ga musulmai da ƙasashensu da mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu.

Manufofin Fassarorin

48 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية