1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla

عَنْ ‌وَرَّادٍ كَاتِبِ الْمُغِيرَةِ بْنِ شُعْبَةَ قَالَ: أَمْلَى عَلَيَّ الْمُغِيرَةُ بْنُ شُعْبَةَ فِي كِتَابٍ إِلَى مُعَاوِيَةَ:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ مَكْتُوبَةٍ: «لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، اللَّهُمَّ لَا مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ، وَلَا مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلَا يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدُّ».

Daga Warrad magatakardar Mugira ɗan Shu'uba ya ce: Mugira ɗan Shu'uba ya yi min shifta ( yana fada ina rubutawa) ta wata wasiƙa zuwa ga Mu'awiyya:
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya tasa ce, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, ba mai bayar da abin da Ka hana, mai wadata wadatarsa bata amfanar da shi (komai) a wajenKa".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 844

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya ta tabbata a gareShi, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, kuma ba mai bayar da abin da Ka hana, kuma mai wadata wadatarsa ba ta amfanar da shi (komai) a wajenKa".
Wato: Ina tabbatar da kalmar tauhidi babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ibada ta gaskiya ina tabbatar da ita ga Allah, kuma ina koreta daga waninSa, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina tabbatar da cewa mulki na haƙiƙa cikakke na Allah ne, dukkanin godiyar wadanda ke sammai da ƙasa abar cancanta ce ga Allah - Maɗaukakin sarki -, yayin da yake Shi mai iko ne a kan dukkan komai, kuma abin da Allah Ya kaddara shi na bayarwa ko hanawa ba mai juyar da shi, kuma a wajenSa wadata ba ta amfanar da ma'abocinta, kaɗai aikinsa nagari ne zai amfanar da shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so yin wannan zikirin a bayan salloli saboda abin da ke ƙunshe a cikinsa na lafazan tauhidi da godiya.
  2. Gaggawa zuwa ga ruko da sunnoni, da kuma yaɗasu.

Manufofin Fassarorin

61 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية