1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ تَرَدَّى مِنْ جَبَلٍ فَقَتَلَ نَفْسَهُ فَهُوَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ يَتَرَدَّى فِيهِ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ تَحَسَّى سُمًّا فَقَتَلَ نَفْسَهُ فَسُمُّهُ فِي يَدِهِ يَتَحَسَّاهُ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ قَتَلَ نَفْسَهُ بِحَدِيدَةٍ فَحَدِيدَتُهُ فِي يَدِهِ يَجَأُ بِهَا فِي بَطْنِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada, wanda ya tsotsi wata gubar sai ya kashe kansa to gubarsa tana hannunsa zai dinga tsotsarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe to ƙarfen zai zama a hannunsa zai dinga cakawa cikinsa shi a cikin wutar Jahannama yana madawwami har abada a cikinta».

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 5778

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi gangancin kashe kansa gargaɗi a duniya cewa za’a yi masa uƙuba a ranar alƙiyama a cikin wutar Jahannama ta irin hanyar da ya yi wa kansa a duniya dan sakamakon da ya dace, wanda ya faɗo daga saman dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wutar Jahannama zai dinga faɗowa a cikinta daga dutsen Jahannama zuwa kwarinta yana madawwami a cikinta, wanda ya kwankwɗi wata guba sai ya kashe kansa da ita to gubarsa tana hannunsa zai dinga kwankwaɗarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya cakawa kansa wani karfe a cikinsa sai ya kashe kansa, to karfensa yana hannunsa zai dinga sukar kansa da shi a cikinsa a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin mutum ya kashe kansa, kuma cewa shi yana daga cikin manyan zunuban da yake cancantar azaba mai raɗaɗi da su.
  2. Abinda ya ambata a cikin hadisin buga misali ne ga wasu daga cikin nau'ikan kashe rai, inba haka ba to ta kowace hanaya ya kashe rai za’a yi masa uƙuba da kwatankwacin abinda ya aikatawa kansa, haƙiƙa faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo a cikin Sahihul Bukhari cewa: «Wanda ya shaƙe kansa zai shaƙe shi a cikin wuta, wanda kuma ya soke kansa to zai sokeshi a cikin wuta».
  3. Nawawi ya ce: Amma faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (To shi yana cikin wutar Jahanama yana madawwami a cikinta har abada); sai aka ce: A cikinsa akwai maganganu, na farkonsu: Cewa shi abin ɗauka ne akan wanda ya aikata hakan yana mai halattawa tare da saninsa da haramcin to wannan kafiri ne, wannan kuma ita ce uƙubarsa. Na biyu: Cewa abin nufi da dawwama ita ce tsawon dadewa da kuma zaman da za'a tsawaita ba wai haƙiƙanin dawwamar ba, kamar yadda ake cewa: Allah Ya dawwamar da mulkin sarki. Na uku: Cewa wannan shi ne sakamakonsa, sai dai (Allah) tsarki ya tabbatar maSa ya daukaka ya yi baiwa sai Ya bada labarin cewa wanda ya mutu yana musulmi ba zai dawwama a cikin wuta ba.
  4. Wannan yana daga babin tabbatar da jinsin uƙubobin lahira ga laifukan duniya, kuma ana fahimta daga gare shi cewa laifin mutum yana kan kansa kamar laifin waninsa ne akan waninsa a zunubi; domin cewa ransa ba mallakinsa bane kai tsaye, kai shi na Allah ne - Maɗaukakin sarki -, ba'a tasarrufi a cikinsa sai da abinda Ya yi masa izini a cikinsa.

Manufofin Fassarorin

40 Yare
EN English Turanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية