1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa ‌Mumini ba zai gusheba a cikin yalwar Addininsa ba, muddin dai bai zubar da jinin da aka haramta masa ba

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَنْ يَزَالَ المُؤْمِنُ فِي فُسْحَةٍ مِنْ دِينِهِ، مَا لَمْ يُصِبْ دَمًا حَرَامًا».

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«‌Mumini ba zai gusheba a cikin yalwar Addininsa ba, muddin dai bai zubar da jinin da aka haramta masa ba».

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 6862

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mumini ba zai gushe ba a cikin yalwar ayyukansa na gari, da fatan samun rahamar Allah da gafararSa da kuma rangwaminSa, har sai idan ya kashe wani mutumin da aka haramta masa kashe shi to haƙiƙa ayyukansa zasu yi masa ƙunci; domin ba zasu iya biyan laifin kisa da kuma zunibinsa mai girma ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girman kisa ba tare da wani haƙƙi ba da kisa na ganganci, domin yana fitar da mumini daga yalwa a cikin Addini zuwa ƙunci.
  2. Jinanen da aka haramta nau'i huɗu ne: 1- Jinin musulmi, shi ne mafi girmansu. 2- Jinin kafirin amana (Zimmi), su ne Yahudawa da Nasara waɗanda aka tabbatar da su akan addininsu a garin Musulunci ta hanyar bada jizya, da zartar da hunce-hukuncen Musulunci a cikinsu. 3- Jinin kafirin da aka yi yarjejeniya da shi (Mu'ahad), sune kafiran da suke a garuruwansu waɗanda a tsakaninmu akwai sulhu cewa ba zamu yaƙesu ba suma ba zasu yaƙemu ba. 4- Jinin kafiri Musta'amani, shi ne kafirin da ake yaƙi da shi wanda tsakaninmu babu alƙawari, sai dai shugaba ko wanda yake mallakar hakan daga mataimakansa ya amintar da shi a lokaci iyakantacce cewa zai shigo garin musulmai.

Manufofin Fassarorin

34 Yare
EN English Turanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية