1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Musulunci ya fara yana baƙo, kuma zai dawo baƙo, aljanna ta tabbata ga baƙi

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«بَدَأَ الْإِسْلَامُ غَرِيبًا، وَسَيَعُودُ كَمَا بَدَأَ غَرِيبًا، فَطُوبَى لِلْغُرَبَاءِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Musulunci ya fara yana baƙo, kuma zai dawo baƙo, aljanna ta tabbata ga baƙi».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 145

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Musulunci ya fara yana baƙo a cikin ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙarancin ma'abotansa, kuma zai dawo yana baƙo saboda ƙarancin wanda zai tsayu da shi, to farin ciki, kuma madalla ga baƙi, da farin ciki da sanyin ido gare su.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bada bayanin kasantuwar baƙuntar Musulunci bayan yaɗuwarsa da kuma shahararsa.
  2. A cikinsa akwai alama daga alamomin Annabci, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari da abinda zai faru a bayansa, sai ya faru kamar yadda ya bada labari da shi.
  3. Falalar wanda ya ƙauracewa ƙasarsa da danginsa; saboda Musulunci, kuma lallai aljanna ta tabbata agare shi.
  4. Baƙi su ne waɗanda suke gyaruwa idan mutane suka ɓaci, kuma sune waɗanda suke gyara abinda mutane suka ɓata.

Manufofin Fassarorin

41 Yare
EN English Turanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية