عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
قَدِمَ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَبْيٌ، فَإِذَا امْرَأَةٌ مِنَ السَّبْيِ قَدْ تَحْلُبُ ثَدْيَهَا تَسْقِي، إِذَا وَجَدَتْ صَبِيًّا فِي السَّبْيِ أَخَذَتْهُ، فَأَلْصَقَتْهُ بِبَطْنِهَا وَأَرْضَعَتْهُ، فَقَالَ لَنَا النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَتُرَوْنَ هَذِهِ طَارِحَةً وَلَدَهَا فِي النَّارِ؟» قُلْنَا: لاَ، وَهِيَ تَقْدِرُ عَلَى أَلَّا تَطْرَحَهُ، فَقَالَ: «لَلَّهُ أَرْحَمُ بِعِبَادِهِ مِنْ هَذِهِ بِوَلَدِهَا».

Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -:
Wasu ribatattu sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga wata mace daga cikin ribatattun nonanta yana zuba tana shayar da ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaro a cikin ribatattun sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mana: «‌Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta?» muka ce: A'a, alhali ita tana da ikon ƙin jefa shi, sai ya ce:«‌Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta».

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 5999

Bayani

An zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wasu ribatattu daga (ƙabilar) Hawazin, sai ga shi a cikinsu akwai wata mace tana neman ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaron da ta ɗauke shi sai ta shayar da shi saboda cutuwa da tayi ta hanyar taruwar nono a cikin hantsarta, sai ta samu ɗanta a cikin ribatattu sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa sahabbansa: Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta? Muka ce: Ba zata jefa shi da yardarta ba har abada. Sai ya ce: Allah Ya fi jin tausayin bayinSa daga wannan matar da ɗanta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Rahamar Allah mai yalwa ce ga bayinSa, kuma Shi Yana nufin alheri da aljanna garesu, da kuma tsira daga wuta.
  2. Fa'idantuwa daga abubuwan dake faruwa da kuma alaƙanta su a kan fadakarwa da kuma koyarwa.
  3. Yana kamata ga mumini ya zama mai kyakkyawan zato ga Allah, kuma kada ya yanke ƙauna tare da tsoron Allah da kuma tabbata akan AddininSa, domin Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Ma'abocin rahama ne mayalwaciya.

Manufofin Fassarorin

35 Yare
EN English Turanci
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية