Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

64lis din Hadisai

lis din Hadisai 64

Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi
Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka
Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyiNa to haƙiƙa na sanar da shi yaƙi, kuma bawa Na bai nemi kusanci gareni da wani abu mafi soyuwa gareNi ba daga abin da na wajabata masa
Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa
Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya
Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku
Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba
Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku
Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura
Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa
Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona
Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama
Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi
Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa
Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba
Lallai cewa wani Bayahude ya zo wajen Annabi sai ya ce da shi ya muhammad, Cewa Allah ya rike Sammai kan Yatsa daya, Kuma Kassai Kan Yatsa daya, kuma Duwatsu kan Yatsa daya, kuma Bushiyu Kan Yatsa daya, Kuma Halittu kan Yatsa daya, sannan ya ce: Ni ne Sarki
Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba
‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu
ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskarSa Mai girma, da sarautarSa daɗaɗɗiya, daga Shaiɗan abin jefewa
Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba?
Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira
Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa
Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?
Wani Malami daga Malaman Yahudawa yazo wajan Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai yace:Ya Muhammad,hakika mun samu cewa Allah zai sanya Sammai akan yatsa,kuma kassai akan Yatsa,kuma Bishiyu akan Yatsa,kuma Ruwa akan Yatsa,kuma Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halittu akan Yatsa,sannan yace:Nine Mamallaki.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan.Sannan ya karanta:"Kuma basu kaddara Allah Hakikanin ikonsa ba, kuma Kasa duka damkarsa ce a Ranar Kiyama"?.Acikin wata Ruwaya ta Muslim:"Da Duwatsu da Bishiyu akan Yatsa,sannan ya girgizasu sannan yace:Nine Mamallaki,nine Allah".Kuma acikin wata Ruwaya ta Buhari:"Zai sanya Sammai akan Yatsa,kuma Ruwa da Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halitta akan Yatsa"
Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu
‌Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana
‌Lallai cewa Allah idan Ya so wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce: Lallai cewa Ni ina son wane to ka so shi, ya ce: Sai Jibril yaso shi
‌Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta
Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci