1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi

عن أُبيِّ بن كعبٍ رضي الله عنه قال:
صلَّى بنا رسولُ الله صلى الله عليه وسلم يومًا الصُّبحَ فقال: «أشاهِد فُلان؟» قالوا: لا، قال: «أشاهِدٌ فُلان؟» قالوا: لا، قال: «إنَّ هاتيَنِ الصَّلاتين أثقَلُ الصَّلَواتِ على المُنافقين، ولو تعلمون ما فيهما لأتيتُمُوهما ولو حَبْوًا على الرُّكب، وإن الصفَّ الأوّلَ على مِثلِ صَفِّ الملائكة، ولو عَلِمتُم ما فضيلتُه لابتَدَرتُموهُ، وإنّ صلاةَ الرجل مع الرجل أزكى من صلاتِه وحدَه، وصلاتَه مع الرجلَين أزكى من صلاتِه مع الرجل، وما كَثُرَ فهو أحبُّ إلى الله تعالى».

Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba wata rana sai ya ce: "Shin wane ya zo ne?" suka ce: A'a, ya ce: "Shin wane ya zo ne?" Suka ce: A'a, ya ce: 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi, kuma cewa sahun farko yana kan kwatankwacin sahun mala'iku, da ace kun san falalarsa da kun yi gaggawarsa. Lallai sallar namiji tare da namiji tafi tsarki daga sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tsarki daga sallarsa tare da namiji ɗaya, abinda ya yawaita to shine mafi soyuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -".

Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shi Sunan Abi Dawud - 554

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba wata rana, sannan ya yi tambaya: Shin wane ya zo wannan sallar da muka yi? Sahabbai suka ce: A'a. Sannan ya ce: Shin wane ya zo ne? ga wani mutumin daban, Suka ce: A'a. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lallai sallar Asuba da Issha'i sune mafi nauyin salloli akan munafukai; dan rinjayar kasala a cikinsu, da kuma ƙarancin faruwar riya garesu, tunda ba'a ganinsu a cikin duhu.
Da kun san yaku muminai abinda ke cikin sallolin Asuba da Issha'i na lada da sakamako mai ƙaruwa - domin lada yana kan gwargwadan wahala - da kun zo su koda da jan ciki ne da tafiya akan hannaye da gwiwowi.
Kuma masu sahu na farko a kusancinsu da liman kamar sahun mala'iku ne a kusancinsu ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da muminai suna sanin abinda ke cikin falalar sahun farko da sun yi tsere gare shi . Kuma lallai sallar namiji tare da namiji ita ce mafi girman sakamako da tasiri a sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tare da namiji ɗaya, Sallar da masallatan suka yi yawa a cikinta ita ce mafi soyuwa ga Allah kuma ta fi lada.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin limamin masallaci ya bibiyi halayen mamu, da tambaya daga wanda ya bai zo ba daga cikinsu.
  2. Lazimtar sallar jam’i musamman ma dai sallar Issha'i da Asuba yana daga alamomin imani.
  3. Girman ladan sallolin Issha'i da Asuba; dan abinda ke cikin zuwa gare su na yaƙar zuciya da nacewa akan ɗa'a, sai ladansu ya zama mafi girma daga wasunsu.
  4. Sallar jama'a tana ƙulluwa ne daga mutum biyu zuwa sama.
  5. Bayanin falalar sahun farko, da kwaɗaitarwa a cikin gaggawa zuwa gare shi .
  6. Falalar yawan jama'a, domin cewa duk lokacin jama'a suka yi yawa ladan yafi yawa.
  7. Ayyuka na gari suna da fifikon lada gwargwadan fifitawar shari'a garesu, da kuma abinda suka siffantu da su na halaye.

Manufofin Fassarorin

53 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية