1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ أَكَلَ ثُومًا أَوْ بَصَلًا، فَلْيَعْتَزِلْنَا -أَوْ قَالَ: فَلْيَعْتَزِلْ- مَسْجِدَنَا، وَلْيَقْعُدْ فِي بَيْتِهِ»، وَأَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أُتِيَ بِقِدْرٍ فِيهِ خَضِرَاتٌ مِنْ بُقُولٍ، فَوَجَدَ لَهَا رِيحًا، فَسَأَلَ فَأُخْبِرَ بِمَا فِيهَا مِنَ البُقُولِ، فَقَالَ قَرِّبُوهَا إِلَى بَعْضِ أَصْحَابِهِ كَانَ مَعَهُ، فَلَمَّا رَآهُ كَرِهَ أَكْلَهَا، قَالَ: «كُلْ فَإِنِّي أُنَاجِي مَنْ لاَ تُنَاجِي». ولِمُسْلِمٍ عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ أَكَلَ مِنْ هَذِهِ الْبَقْلَةِ، الثُّومِ - وقَالَ مَرَّةً: مَنْ أَكَلَ الْبَصَلَ وَالثُّومَ وَالْكُرَّاثَ فَلَا يَقْرَبَنَّ مَسْجِدَنَا، فَإِنَّ الْمَلَائِكَةَ تَتَأَذَّى مِمَّا يَتَأَذَّى مِنْهُ بَنُو آدَمَ».

Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa", kuma cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa daga maɓungura ƙasa, sai ya ji wari daga gareta, sai ya yi tambaya sai aka ba shi labarin abinda ke cikinta na maɓungura ƙasa, sai ya ce ku kusantar da ita ga wani daga sahabbaina wanda ke tare da shi, lokacin da ya ganta sai ya ƙyamaci cinta, ya ce: "Ka ci domin cewa ni ina ganawa da wanda ba ka ganawa (da shi)". A riyawayar Muslim daga Jabir ɗan Abdullahi, daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci daga waɗannan maɓungura ƙasan, tafarnuwa - wani lokacin kuma ya ce: Wanda ya ci albasa da tafarnuwa da algarif to kada ya kusanci masallacinmu, domin mala'iku suna cutuwa da abinda 'ya'yan Adam suke cutuwa da shi".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 855

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya ci tafarnuwa ko albasa zuwa masallaci, dan kada ya cutar da 'yan uwansa daga waɗanda suka halarci sallar jam’i da warinsu, shi hanine na tsarkakewa daga zuwa masallaci, ba dan an hana cinsu ba: domin cewa su suna daga abubuwan da aka halatta, haƙiƙa an zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa, lokacin da ya shaƙi wari a cikinta kuma aka ba shi labarin abinda ke cikinta sai ya hanu daga cinta ya kuma kusantar da ita ga wani daga sahabbansa dan ya ci daga gareta, sai ya kyamaci ci dan koyi da shi, lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gan shi ya ce: Ka ci; domin cewa ni ina ganawa da Mala’iku idan sun zo da wahayi.
kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'iku suna cutuwa daga warin da ake ƙi, kamar yadda mutane suke cutuwa daga gare shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hanin zuwa masallaci ga wanda ya ci tafarnuwa, ko albasa, ko algarif.
  2. Ana riskar da waɗannan abubuwan, dukkan abinda yake da warin da masallata suke cutuwa daga gare shi, kamar warin taba da wiwi da makancin hakan.
  3. Illar hanin “wari”, idan ya gushe da yawan dafuwa ko wanin hakan; to karhancin ya gushe.
  4. Karhancin cin waɗannan abubuwan ga wanda zuwa sallah a masallaci ya wajaba akansa; dan kada jam'i ya wuce shi a cikin masallaci, muddin dai bai ci ba dan dabara akan kin halarta, to (cin) ya haramta.
  5. Hanuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga cin tafarnuwa da makancinsa, badan haramcinsa ba ne, kawai dan ganawarsa ne da (mala'ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -.
  6. Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da bayanin sababinsa; dan wanda ake magana ya nutsu da sanin hikimar.
  7. Alkali ya ce: Malamai sun ƙiyasta wanin masallaci akan wuraren haɗuwa dan yin sallah, kamar wurin sallar idi da jana'iza da makancinsu daga wuraren taruwa dan yin ibadu, haka nan wuraren taruwa na ilimi da zikiri da walimomi da makancinsu, ba za'a riskar da kasuwanni da wasunsu da su ba.
  8. Malamai sun ce: A cikin wannan hadisin akwai dalili akan hana cin tafarnuwa da makamancinta daga shiga masallaci - koda ya kasance ba kowa - domin shi guri ne na mala'iku, kuma saboda gamewar hadisan.

Manufofin Fassarorin

51 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية