1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ غَدَا إِلَى الْمَسْجِدِ أَوْ رَاحَ أَعَدَّ اللهُ لَهُ فِي الْجَنَّةِ نُزُلًا، كُلَّمَا غَدَا أَوْ رَاحَ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:
"Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 669

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya zo masallaci dan yin ibada ko ilimi ko wanin hakan daga manufofin alheri a kowanne lokaci albishir; a farkon yini ko ƙarshensa da cewa Allah haƙiƙa ya tanadar masa da wani wuri da garar baƙi a cikin aljanna, duk lokacin da ya zo masallaci a dare ko yini.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar tafiya zuwa masallaci, da kwaɗaitarwa akan kiyayewa akan yin sallar jam'i a cikinsa, da yawa mai ƙin zuwa masallaci alheri da falala da lada da garar baƙi suke wuce shi waɗanda Allah - alherinSa ya yawaita Ya ɗaukaka - ga masu nufin ɗakinSa.
  2. Idan mutane sun kasance suna girmama wanda ya zo gidajensu, suna gabato masa da abinci, to Allah - alherinSa ya yawaita Ya ɗaukaka - Shi ne Mafi kyauta daga halittarSa! wanda ya nufi ɗakinSa zai girmama shi, kuma Allah Zai tanadar masa da masauki mai girma kuma babba.
  3. Farin ciki da nishaɗi da tafiya masallatai; domin ana tanadar masa da masauki a duk lokacin ya wayi gari ko ya kai maraice da adadin tafiyarsa.

Manufofin Fassarorin

51 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية