1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَسْرِعُوا بِالْجِنَازَةِ، فَإِنْ تَكُ صَالِحَةً فَخَيْرٌ تُقَدِّمُونَهَا، وَإِنْ يَكُ سِوَى ذَلِكَ، فَشَرٌّ تَضَعُونَهُ عَنْ رِقَابِكُمْ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 1315

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yin gaggawa da shirya jana'iza da yi mata sallah da kuma binneta; idan jana'izar ta kasance ta garice to alheri ne, kuke gabatarwa gare shi na ni'imar ƙabari, idan kuma ta kasance koma bayan haka ne to sharri ne kuke saukewa daga wuyayenku.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ibnu Hajar ya ce: An so yin gaggawa, sai dai ta inda abinda ake jin tsoron faruwar ɓarna ga mamaci, ko wahala akan mai ɗaukar ko mai rakiyar ya tsanananta matuƙa.
  2. An ƙayyade gaggawar da idan mutuwar bata zama fuj'a ba wacce ake jin tsoron ta zama suma ce, to yana kamata kada a binneta har sai an tabbatar da mutuwarsa, ko ya zama akwai wata maslaha a cikin jinkirta shi, na yawaitar masallata, ko halartar 'yan uwansa, kuma ba'a jin tsoron ta ɓaci.
  3. Kwaɗaitarwa akan yin gaggawa da jana'iza dan maslahar mamaci idan ya kasance ɗan aljanna ne, ko dan maslahar 'yan rakiya idan ya kasance ɗan wuta ne.
  4. Nawawi ya ce: Ana ɗauka daga gare shi (wannan Hadisin) barin abokantakar da mutanen banza waɗanda ba mutanen kirki ba.

Manufofin Fassarorin

40 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية