1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa ‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce

عَن أُمِّ الدَّرْدَاءِ وَ أَبِي الدَّرداءِ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ:
«دَعْوَةُ الْمَرْءِ الْمُسْلِمِ لِأَخِيهِ بِظَهْرِ الْغَيْبِ مُسْتَجَابَةٌ، عِنْدَ رَأْسِهِ مَلَكٌ مُوَكَّلٌ كُلَّمَا دَعَا لِأَخِيهِ بِخَيْرٍ، قَالَ الْمَلَكُ الْمُوَكَّلُ بِهِ: آمِينَ وَلَكَ بِمِثْلٍ».

Daga Ummu al-Darda'i da Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbara agare shi - ya kasance yana cewa:
«‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2733

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa musulmi a bayan idon wanda aka yi wa addu'ar abar karɓa ce; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a cikin ikhlasi, kuma lallai cewa a wajen kan mai addu'ar akwai wani Mala'ikan da aka wakilta, a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce; Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin abinda ka roƙa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan kyautatawa muminai sashinsu ga sashi ko da da addu'a ne.
  2. Addu'a a ɓoye tana nuni a bayyane akan gaskiyar imani da kuma 'yan uwantaka.
  3. Ƙayyade addu'a da cewa a ɓoye; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a ikhlasi (wato yi domin Allah) da kuma halartowar zuciya.
  4. Daga cikin sabubban amsa addu'a akwai musulmi ya yi wa ɗan'uwansa musulmi addu'a a ɓoye.
  5. Nawawi ya ce; Falalar addu'a ga ɗan'uwansa musulmi a ɓoye, da a ce zai yi wa jama'ar musulmai addu'a to wannan falalar zata tabbata, da kuma a ce zai yi addu'a ga jumlar musulmai to zance mabayyani shi ne samuwar (falalar), wani daga cikin magabata na gari ya kasance idan yana so ya yi wa kansa addu'a sai ya yi wa ɗan'uwansa addu'a da wannan addu'ar; domin cewa ita za'a amsata, kuma zai samu kwatankwacinta.
  6. Bayanin wasu daga cikin ayyukan Mala'iku, kuma cewa daga cikinsu akwai wanda Allah Ya wakilta shi ga wannan aikin.

Manufofin Fassarorin

37 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية