1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai

عن عائشة أم المؤمنين وعبد الله بن عباس رضي الله عنهما قالا:
لَمَّا نَزَلَ بِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ طَفِقَ يَطْرَحُ خَمِيصَةً لَهُ عَلَى وَجْهِهِ، فَإِذَا اغْتَمَّ بِهَا كَشَفَهَا عَنْ وَجْهِهِ، فَقَالَ وَهُوَ كَذَلِكَ: «لَعْنَةُ اللَّهِ عَلَى اليَهُودِ وَالنَّصَارَى، اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ» يُحَذِّرُ مَا صَنَعُوا.

Daga Nana A'isha da Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - sun ce:
Lakacin da (wafati) ya saukar wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara yana rufe fuskarsa da wani mayafinsa, idan ya ji ya yi masa tsanani sai ya yaye shi daga fuskarsa, sai ya ce yana hakan: "Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai" yana gargaɗi game da abin da suka aikata.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 435

Bayani

Nana A'isha da Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - suna ba mu labarin cewa lokacin da wafati ya halartowa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara sanya wani yanki na riga a kan fuskarsa, idan numfashi ya wuyata a gareshi saboda magagin mutuwa, sai ya gusar da shi daga fuskarsa, sai ya faɗa a wannan halin mai tsanani: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, ya koresu daga rahamarSa; domin su sun gina masallatai a kan kaburburan Annabawansu, da ba don haɗarin al'amarin ba da bai ambace shi a irin wannan lokacin ba, saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana al'ummarsa da kamanceceniya da wannan aikin; domin yana daga aikin Yahudawa da Nasara, kuma hanya ce da za ta kai zuwa ga shirka da Allah - mai girma da ɗaukaka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga riƙon kaburburan Annabawa da salihai masallatan da za a dinga sallah a cikinsu; domin hakan hanya ce zuwa shirka.
  2. Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama kaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa shirka.
  3. Halaccin la'antar Yahudawa da Nasara, da wanda ya aikata irin aikinsu na gini a kan kaburbura da kuma rikonsu masallatai.
  4. Gini a kan kaburbura yana daga dabi’un Yahudawa da Nasara, a cikin Hadisin akwai hani daga kamanceceniya da su.
  5. Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.

Manufofin Fassarorin

61 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية