1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku

عَنْ مُصْعَبِ بْنِ سَعْدٍ قَالَ: رَأَى سَعْدٌ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ لَهُ فَضْلًا عَلَى مَنْ دُونَهُ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«هَلْ تُنْصَرُونَ وَتُرْزَقُونَ إِلَّا بِضُعَفَائِكُمْ».

Daga Mus'ab ɗan Sa'ad ya ce: Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ga cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku".

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 2896

Bayani

Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya yi zatan cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi daga raunana saboda gwarzantakarsa da makamancin haka! Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin ana taimakonku ne kuma ana azirtaku ai sai saboda raunananku ta hanyar addu'o'insu da sallalolinsu da ikhlasinsu; domin su a galibi su ne mafi tsananin ikhlasi a cikin addu'a, kuma mafi yawan khushu'i a cikin ibada dan wofintar zuciyarsu daga rataya da ƙawace-ƙawacen duniya.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan tawali'u da hana rena wasu daban.
  2. Ibnu Hajar ya ce: Idan mai ƙArgo yana rinjaya saboda gwarzantakara, to shi mai rauni yana rinjaya saboda falalar addu'arsa da kuma ikhlasinsa.
  3. Kwaɗaitarwa akan kyautatawa talakawa da basu haƙƙoƙinsu, domin hakan yana daga sabubban rahamar Allah gareka da kuma taimakonSa.

Manufofin Fassarorin

40 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية