1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr

عن عائشةَ أمِّ المؤْمنِين رضي الله عنها قالت:
لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَيْءٍ مِنَ النَّوَافِلِ أَشَدَّ مِنْهُ تَعَاهُدًا عَلَى رَكْعَتَيِ الفَجْرِ.

Daga Nana Aisha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce :
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 1169

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimta da kuma kiyaye wa ba akan wani abu na nafiloli sama da raka'o'i biyu ratibai na kafin sallar Asuba ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Nafilolin sallah sune waɗanda ba farillai ba na ayyukan ɗa'a, kuma abin nufi a nan: Sunnoni ratibai masu bin farillai.
  2. Sunnoni ratibai: Raka'o'i biyu kafin Asuba, da raka'o'i huɗu kafin Azahar da biyu bayanta, da raka'o'i biyu bayan Magariba, da raka'o'i biyu bayan Issha'i.
  3. Ana sallatar ratibar Asuba a halin zaman gida da kuma tafiya, saɓanin ratibar Azahar da Magariba da Issha'i, ba a yin su sai a halin zaman gida.
  4. An so, so mai ƙarfi a raka'o'i biyun Asuba, saboda haka ba ya kamata a yi sakaci da su.

Manufofin Fassarorin

37 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية