1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai ya yi fitsari akan tufafinsa, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan bai wanke shi ba

عَنْ أُمِّ قَيْسٍ بِنْتِ مِحْصَنٍ رَضيَ اللهُ عنها:
أَنَّهَا أَتَتْ بِابْنٍ لَهَا صَغِيرٍ لَمْ يَأْكُلِ الطَّعَامَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَجْلَسَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجْرِهِ، فَبَالَ عَلَى ثَوْبِهِ، فَدَعَا بِمَاءٍ، فَنَضَحَهُ وَلَمْ يَغْسِلْهُ.

Daga Ummu Kais Bint Mihsan -Allah Ya yarda da ita -:
Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai ya yi fitsari akan tufafinsa, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan bai wanke shi ba.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 223

Bayani

Ummu Kais bintu Mihsan - Allah Ya yarda da shi - ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani ɗanta wanda bai fara cin abinci ba saboda ƙanƙantar shekarunsa, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai yaron ya yi fitsari akan tufafinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan akan tufafinsa bai wanke tufafin ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kyawawan Ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabata agare shi - mai girma, da kuma tawali'unsa mai yawa.
  2. An so kyautata kyakkyawar mu'amala da tawali'u da tausasawa ga ƙananan yara, da gyara zukatan manya ta hanyar girmama ƙananan yaransu da kuma zaunar da su a ƙirji, da makamancin haka.
  3. Najasar fitsarin yaro ko da bai fara cin abinci daomin sha'awa ba.
  4. Aikin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ana kiransa yayyafi, kuma ya keɓanci ƙaramin yaro ne wanda bai fara cin abinci ba, amma mace to babu makawa sai an wanke fitsarinta koda ta kasance ƙarama ce.
  5. Bahayar yaro wanda yake cin abinci ta hanyar tsotson nonon mahaifiyarsa to babu makawa a cikin hakan sai an wanke kamar sauran najasa.
  6. Babu makawa a wankewar daga wani al'amari na ƙari akan sanya ruwan.
  7. Abin da ya fi yin gaggawa da tsaftace bigiren najasar; dan gaggawa a tsarkaka daga kabasin, kuma dan kada a manta.

Manufofin Fassarorin

33 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TH ไทย Yaran Tailand
AS অসমীয়া Asami
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية