1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْخُلُ الْخَلَاءَ، فَأَحْمِلُ أَنَا وَغُلَامٌ نَحْوِي إِدَاوَةً مِنْ مَاءٍ وَعَنَزَةً فَيَسْتَنْجِي بِالْمَاءِ.

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa.

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 271

Bayani

Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya kasance da wani mai yin hidima sa'ansa a shekaru suna bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya fita dan biyan buƙatarsa, suna ɗaukar masa sanda mai kai irin kan goron mashi dan ya sanyata kariya da zai rataya wani abu a kanta yana mai suturtawa ko kuma sutura ga sallarsa, kuma suna ɗaukar masa ƙaramar ƙwarya na fata wacce take a cike da ruwa, idan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gama biyan buƙatarsa sai ɗaya daga cikinsu ya ba shi ƙwaryar, sai ya yi tsarki da ruwa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Musulmi ya yi tanadin ruwan tsarki a lokacin biyan buƙata; dan kada ya buƙatar da shi zuwa tashi sai ya ɓata jikinsa.
  2. Kiyaye al'aura a lokacin biyan buƙata dan kada wani ya ganta; domin kallon al'aura haramun ne, ya kasance yana kafa sanda a ƙasa kuma yana shinfiɗa tufa mai suturtawa a kanta.
  3. Koyar da yara ladubban Musulunci da kuma tarbiyantar da su akanta; dan su gaje su (su saba da su).

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية