1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ أَهْوَنَ أَهْلِ النَّارِ عَذَابًا مَنْ لَهُ نَعْلَانِ وَشِرَاكَانِ مِنْ نَارٍ، يَغْلِي مِنْهُمَا دِمَاغُهُ كَمَا يَغْلِ الْمِرْجَلُ، مَا يَرَى أَنَّ أَحَدًا أَشَدُّ مِنْهُ عَذَابًا، وَإِنَّهُ لَأَهْوَنُهُمْ عَذَابًا».

Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu"

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 213

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba a ranar lahira wanda yake da takalma biyu da igiyoyi biyu ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa saboda zafinsu, kamar yadda tukunyar tagulla take tafarfasa, kuma ba ya ganin wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi ne mafi sauƙin azabarsu, hakan dan azabar jiki da ta rai su haɗu a kansa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tsoratar da masu saɓo da kafirai daga tsoron wannan azabar a cikin wuta; dan su nisanci abinda zai kai zuwa gareta.
  2. Banbacin matsayin masu shiga wuta gwargwadan mummunar ayyukansu.
  3. Tsananin azabar wuta, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kuɓutar da mu daga gareta.

Manufofin Fassarorin

49 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية