1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
أَلَسْتُمْ فِي طَعَامٍ وَشَرَابٍ مَا شِئْتُمْ؟ لَقَدْ رَأَيْتُ نَبِيَّكُمْ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَا يَجِدُ مِنَ الدَّقَلِ مَا يَمْلَأُ بِهِ بَطْنَهُ.

Daga Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba.

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2977

Bayani

Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - yana ambatawa mutane abinda suke a cikinsa na ni'ima, kuma su basu gushe ba suna yadda suke so a cikin abin cin da abin sha, sannan ya bada labarin halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi bai kasance yana samun dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi saboda yunwa ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin halin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa na gudun duniya.
  2. Kwaɗaitarwa akan gudun duniya da kuma ƙarantuwa daga gareta da kuma koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Tunatar da mutane ni'imomin da suke a cikinsu da kuma kwaɗaitarwa akan godewa Allah a kansu.

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية