1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahman - Mai girma da ɗaukaka - su duka hannayensa biyun na dama ne

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«إِنَّ الْمُقْسِطِينَ عِنْدَ اللهِ عَلَى مَنَابِرَ مِنْ نُورٍ، عَنْ يَمِينِ الرَّحْمَنِ عَزَّ وَجَلَّ، وَكِلْتَا يَدَيْهِ يَمِينٌ، الَّذِينَ يَعْدِلُونَ فِي حُكْمِهِمْ وَأَهْلِيهِمْ وَمَا وَلُوا».

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahman - Mai girma da ɗaukaka - su duka hannayensa biyun na dama ne, waɗanda suke adalci a hukuncinsu da iyalansu da abin da suka jiɓinta".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 1827

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa waɗanda suke hukunci da adalci da gaskiya a tsakanin mutane waɗanda suke ƙarƙashin shugabancinsu da hukuncinsu da iyalansu, cewa su za su zauna a kan abubuwan zama maɗaukaka haƙiƙa an haliccesu daga haske, don girmamawa garesu a ranar al-ƙiyama. Waɗannan munbarorin suna daman Ubangiji Al-Rahman, kuma su duka hannayensa biyun na dama ne.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar adalci da kwaɗaitarwa a kansa.
  2. Adalci mai gamewa ne ya tattaro dukkanin shugabanci da hukunci a tsakanin mutane, har adalci a tsakanin ma'aurata da 'ya'ya da sauransu.
  3. Bayanin matsayin masu adalci a ranar al-ƙiyama.
  4. Banbance-banbancen matsayiyyikan ma'abota imani a ranar al-ƙiyama kowanne da gwargwadon aikinsa.
  5. Salon kwaɗaitarwa yana daga salon kiran da zai kwaɗaitar da wanda ake kira a aikin ɗa'a.

Manufofin Fassarorin

68 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
EL Ελληνικά اليونانية
AK Akan الأكانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
LN Lingala اللينجالا
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
RN Kirundi الكيروندي
YAO Yao الياو
KMR Kurmancî الكرمنجية