1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«أَحَبُّ الْبِلَادِ إِلَى اللهِ مَسَاجِدُهَا، وَأَبْغَضُ الْبِلَادِ إِلَى اللهِ أَسْوَاقُهَا».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 671

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi soyuwar gurare a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka - sune masallatan garuruwan; domin su wuraran ayyukan biyayya ga Allah ne, kuma ginshiƙansu akan tsoron Allah ne. Kuma mafi ƙin garuruwa a wajen Allah sune kasuwanninsu; domin cewa galibi guri ne na algus da yaudara da riba da rantse-rantse akan ƙarya, da saɓa alƙawari, da bijirewa ambatan Allah.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Alfarmar masallatai da gurarensu; domin su gidajen da ake ambatan Allah da yawa ne a cikinsu.
  2. Kwaɗaitarwa akan lazimtar masallatai, da yawan kaikawo zuwa garesu, dan neman soyayyar Allah - Maɗaukakin sarki - da yardarSa, da kuma ƙaranta kaikawo zuwa ga kasuwanni, sai dan buƙata; dan nisanta daga faɗawa cikin sabubban ƙiyayyar (Allah).
  3. Imam Nawawi ya ce: Masallatai gurare ne na saukar rahama, kasuwanni kuwa kishiyarsu ne.

Manufofin Fassarorin

37 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية