1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«أَتَدْرُونَ مَا الْغِيبَةُ؟»، قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «ذِكْرُكَ أَخَاكَ بِمَا يَكْرَهُ»، قِيلَ: أَفَرَأَيْتَ إِنْ كَانَ فِي أَخِي مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «إِنْ كَانَ فِيهِ مَا تَقُولُ فَقَدِ اغْتَبْتَهُ، وَإِنْ لَمْ يَكُنْ فِيهِ فَقَدْ بَهَتَّهُ».

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:
"Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi", aka ce: Shin kana ganin in ya kasance akwai abin da nake faɗa a kan ɗan uwana fa? sai ya ce: "Idan ya kasance a cikinsa akwai abin da kake faɗa, to, haƙiƙa ka yi gibarsa, idan babu (abin da kake faɗa) a cikinsa, to, haƙiƙa ka ƙirƙirar masa ƙarya".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2589

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haƙiƙanin gibar da aka haramta, ita ce: Ambaton musulmi mai gibar da abin da yake ki, daidai ne ya kasance daga siffofinsa ne na halitta ko na ɗabi'a, kamar: Mai ido ɗaya mai yawan algus maƙaryaci, da makamancin hakan daga siffofin zargi, ko da waɗannan siffofin sun kasance samammu ne a gareshi.
Amma idan babu siffar a tare da shi, to, wannan ya fi tsanani daga giba, shi ne ƙirƙirar ƙarya, wato: Ƙirkirar abin da babu a tare da shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ta inda yake jefa mas'aloli ta hanyar tambaya.
  2. Kyakkyawan ladabin sahabbai tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yayin da suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani.
  3. Faɗin wanda aka tamabaya abin da bai sanshi ba; Allah ne mafi sani.
  4. Karewar shari'a ga zamatakewa ta hanyar kare haƙƙoƙi da 'yan uwantaka a tsakaninsu.
  5. Giba abar haramtawa ce sai a wasu halaye dan maslaha; daga hakan akwai: Tunkuɗe zalunci, ta yadda wanda aka zalunta zai ambaci wanda ya zalunceshi ga wanda zai iya karɓa masa haƙƙinsa, sai ya ce: Wane ya zalunceni, ko ya yi min kaza, daga ciki akwai: Shawara a al'amarin aure ko tarayya ko maƙotaka, da makancin hakan.

Manufofin Fassarorin

68 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
JA 日本語 Japananci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
FF Fulfulde الفولانية
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
BG Български البلغارية
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
EL Ελληνικά اليونانية
AK Akan الأكانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
LN Lingala اللينجالا
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
RN Kirundi الكيروندي
YAO Yao الياو
KMR Kurmancî الكرمنجية