1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa "Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «يقول الله تعالى: أَنَا مَعَ عَبْدِي مَا ذَكَرَنِي وَتَحَرَّكَتْ بِي شَفَتَاهُ».

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"

Ingantacce ne ta wani bangaren Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Bukhari Ya Rawaito shi Mu'allak amma ta Sigar Yankewa - Ahmad ne ya rawaito shi

Bayani

Hadisin yana nuna cewa duk wanda ya tuna Allah to Allah zai kasance kusa da shi, kuma zai kasance tare da shi a kowane Al-amuransa, Saboda zai datar da shi kuma ya shirye shi kuma ya taimake shi ya amsa Addu'arsa, kuma Ma'anar wannan Hadisin ta zo a cikin wani hadisin a cikin sahihul Bukhari Manzon Allah ya ce: "Ni ina inda Bawa na ya Zace ni kuma ni ina tare da shi a duk lokacin da ya anbaceni a , idan ya anbaceni cikin Ransa to zan anbace shi cikin raina, in kuma ya anbace ni cikin Mutane zan anbace shi cikin Mutanen da suka fi nasa Al-kairi

Manufofin Fassarorin

16 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese