1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci

عَنْ عَبْدُ اللَّهِ بْنُ سَلَامٍ رضي الله عنه قَالَ: لَمَّا قَدِمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْمَدِينَةَ انْجَفَلَ النَّاسُ قِبَلَهُ، وَقِيلَ: قَدِمَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَدِمَ رَسُولُ اللَّهِ، قَدِمَ رَسُولُ اللَّهِ، ثَلَاثًا، فَجِئْتُ فِي النَّاسِ لِأَنْظُرَ، فَلَمَّا تَبَيَّنْتُ وَجْهَهُ، عَرَفْتُ أَنَّ وَجْهَهُ لَيْسَ بِوَجْهِ كَذَّابٍ، فَكَانَ أَوَّلُ شَيْءٍ سَمِعْتُهُ تَكَلَّمَ بِهِ أَنْ قَالَ:
«يَا أَيُّهَا النَّاسُ، أَفْشُوا السَّلَامَ، وَأَطْعِمُوا الطَّعَامَ، وَصِلُوا الْأَرْحَامَ، وَصَلُّوا بِاللَّيْلِ وَالنَّاسُ نِيَامٌ، تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ بِسَلَامٍ».

Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso Madina sai mutane suka fuskanto gare shi, aka ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, sau uku. Sai na zo a cikin mutane dan inyi kallo, lokacin da na gane fuskarsa, sai nasan cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci bace, farkon abinda na fara jinsa ya yi magana da shi cewa ya ce:
"Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".

Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi Sunanu Ibn Majah - 3251

Bayani

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina, mutane suka ganshi sai suka fuskanci inda yake suna gaggawa, daga waɗanda suka fuskanci inda yake Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya kasance daga Yahudawa, lokacin da ya ganshi sai ya san cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci ba ce; dan abinda ya bayyana gare shi na haske da kyau da kwarjini na gaskiya. Ya kasance farkon abinda ya ji shi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kwaɗaitar da mutane akan ayyukan da zasu zama sababin shiga aljanna, daga cikinsu:
Na farko: Yaɗa gaisuwa da bayyanar da ita da yawaita ta ga wanda ka sani da wanda ma baka sani ba.
Na biyu: Ciyar da abinci ta hanyar sadaka da kyauta da tarbar baƙi.
Na uku: Sadar da zumunci ga wanda zumunci ko kusanci ya ƙullu tsakaninka da su ta ɓangaren uba ko uwa.
Na huɗu: Sallar nafila tsayuwar dare alhali mutane suna bacci.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so yaɗa gaisuwar sallama tsakanin musulmai, amma wanda ba musulmi ba ba'a fara masa da sallama, idan ya yi sallama da faɗin: Assalamu alaikum, sai a mayar masa da faɗin: Wa'alaikum.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية